Tsohon mataimakin ciyaman na PDP Ishola Filani ya rasu yana da shekaru 71
Tsohon mataimakin shugaban jamiyyar PDP na kasa, Cif Ishola Filani ya mutu.
Cif Filani wanda ya kuma kasance shugaban PDP na Kudu maso yamma tsakanin 2012 da 2014, ya rasu a ranar Alhamis, 5 ga watan Afrilu a Landan, jaridar The Nation ta ruwaito.
Filani, wanda ya kasance tsohon sakataren labaran jam’iyyar Democratic Party (SDP) a jumhuriya ta uku ya rasu yana da shekaru 71.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan Legit.ng ta kawo labarin mutuwar wani dan majalisa mai wakiltan Katsina ta arewa Sanata Mustapha Bukar.
KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta kare Buhari akan amincewa da bayar da $1bn na tsaro
Ya rasu a ranar Laraba bayan yar gajeriyar rashin lafiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng