Wasu miyagun mutane sun rataye wata budurwa a gidan iyayenta dake jihar Kano
Rundunar Yansandan jihar Kano ta sanar da rasuwar wata yar buduwar, Khadija a gidansu dake layin Dabo, a unguwar Kurna dake cikin garin Kano, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a yammacin ranar Alhamis, jim kadan bayan mahaifiyarta ta bar yarinyar a gida, ta shiga makwabta don su gaisa, shigarta ke da wuya, ba tafi mintuna 30 ba sai ta ji ana rafka ihu.
KU KARANTA: Tsohon shugaban kasa ya gurgfana gaban Kotu don amsa tuhume tuhumen cin hanci da rashawa
Mahaifiyar ta bayyana ma majiyar Legit.ng cewa ta fita gida ne yayin da da suke zaune tare da yarinyar suna hira a yayin da ta daura sanwar dare, ta cigaba da cewa jin ihun ke da wuya, sai ta fito zuwa gida a guje, inda ta tarar da mutane sun mamaye kofar gidansu.
Ganin hakan ya sanya ta kutsa kai cikin gida, inda tayi karo da gawart diyar ta a rataye, a lokacin da jama’a ke koakrin sauko da gawarta, nan take ta fashe da kuka.
Mahaifin Khadija ya bayyana cewa sun kadu matuka da wannan bala’I da ya gamu da shi, ya kara da cewa su dai har yanzu basu san wanda ya kashe mudu diya ba, ita ta kashe kanta, ko wani ne ya kasheta? Allahu A’alamu.
Zuwa yanzu dai rundunar Yansandan jihar Kano, reshen rijiyar Lemu sun garzaya da gawar Khadija zuwa Asibiti, don gudanar da bincike game da mutuwarta ta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng