2019: An saki wani bidiyo a Ingila da ba zayyi wa Buhari da APC dadi ba

2019: An saki wani bidiyo a Ingila da ba zayyi wa Buhari da APC dadi ba

Bidiyo daga Cambridge Analytica mai nuna hotunan Muhammadu Buhari wai yana karfafa da nuna goyon baya ga Sharia wanda zai iya harzukar da masu mabanbancin ra'ayi kuma ya daidaita da ra'ayin sojojin musulunci ya bayyana.

2019: An saki wani bidiyo a Ingila da ba zayyi wa Buhari da APC dadi ba
2019: An saki wani bidiyo a Ingila da ba zayyi wa Buhari da APC dadi ba

Kasashen hadin kan turai, sun saki bidiyon adawa ga Buhari.

Bidiyo daga Cambridge Analytica masu tatsar bayanan sirri da kwarmata shi, mai nuna hotunan Muhammadu Buhari wai yana karfafa da nuna goyon baya ga Sharia wanda zai iya harzukar da masu mabanbancin ra'ayi kuma ya daidaita da ra'ayin sojojin musulunci ya bayyana.

Wallafawar jaridar Guardian ta Birnin Landan, bidiyon ya nuna abubuwan da suke faruwa zagaye da zaben shugaban kasa na shekara ta 2011.

An samo shi ne daga mai hura husur, wato mai kwarmato Christopher Wylie wanda ya tura bidiyon ga MPs na turai.

A satin da ya wuce, Wylie, tsohon ma'aikaci a Cambridge Analytica yace "Cambridge Analytica ta tura bidiyon wanda daga baya aka hana saka shi a yanar gizo saboda yanayin hotunan da ya kunsa sun sabawa dokokinsu. AIQ ma ta firgita da shi. Bidiyo ne mara kyan gani. Sun sa mishi suna da "Bidiyon kisa"

DUBA WANNAN: Tallafin man fetur ya kai Tiriliyan 1.4 a kasar nan - Kachikwu

An so a sami yaduwar bidiyon a Najeriya ne don tsorata masu dangwala kuri'a. Ya kunshi hotunan cirewa mutane gabobi, yanke makogwaron mutane, mutane cikin jini har dai daga karshe su mutu. Wasu ma da ransu aka birnesu.

"Daukacinshi dai na adawa ga musulunci ne, da sakonnin masu tsoratarwa masu nuna rashin son zaman lafiya na addinin Islama." Inji Wylie.

Wylie ya kara da cewa Cambridge Analytica ta bada umarni ga AIQ, da masu kula da hotunan fim na Canada dasu adana bidiyon domin masu zabe lokacin kashen din zaben shugabancin kasar Najeriya.

Shugaba Buharin dai ya musanta a lokuta da dama cewa bashi da wata ajanda ta Musuluntar da Najeriya, kuma da alama wannan bidiyo so ake a tadiye kafarsa da ita a zabukan 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: