Ilimin Boko a Arewa: Dalibai 28 ne kadai suka zauna jarrabawar common entrance a jihar Zamfara

Ilimin Boko a Arewa: Dalibai 28 ne kadai suka zauna jarrabawar common entrance a jihar Zamfara

MUTUM 28 NE KADAI SUKAYI RIJISTAR ZANA JARABAWAR SHIGA SAKANDIRE A ZAMFARA

A ranar laraban nan data gabata ministan ilimi Adamu Adamu yace gwamnatin tarayya ta nuna damuwar ta akan karancin dalibai da sukayi rigista domin zana jarabawar shiga sakandire na makarantu 104 dake jihar.

Ilimin Boko a Arewa: Dalibai 28 ne kadai suka zauna jarrabawar coomon entrannce a Zamfara
Ilimin Boko a Arewa: Dalibai 28 ne kadai suka zauna jarrabawar coomon entrannce a Zamfara

Mai magana da yawun hukumar ilimi Mrs Priscillia Uhuoma a abuja tace dalibai 28 kadai sukayi rijistar zana jarabara ta shekarar bana a garin Zamfara.anyi kira ga gwamnatocin jaha,shugabannin makarantu da suyi kokari wajen ganin anyi rigistar yanda ya kamata.ya kara da cewar an bada damar barin kofar yin rigistar a bude har zuwa 13 ga afrilu.

Mal. Adamu yace rahoton da suka samu daga ganawar da masu ruwa da tsaki akan harkar sukayi ya nuna cewa jahar Taraba,Kebbi da Zamfara su ne sukafi karancin daliban da suka yi rigistar jarabawar.Jahar Taraba tana da 95 yayin da kebbi keda 50.

Shugaban hukumar zana jarabawar ta samun shiga makarantu 104 dake kasar wanda za'a zana ranar asabar 14 ga watan afrilu ya nuna alhininsa akan karancin yin rigistar da aka samu.

A bangaren sa ya bayyana wanda sukayi rigistar a shekarar 2018 sun tsaya ne a adadin 71,294 akan 80,421 da suka zana a shekarar data gabata.

DUBA WANNAN: An kashe almajiri an farde masa ciki

Rahoton ya bayyana garuruwan da sukafi yawan wadanda sukayi rigistar.Legas tana da dalibai 24,465, Abuja na da 7,699,Sai jihar rivers dauke da dalibai 4,810.A daya hannun kuma jahohin da sukafi karancin dalibai sun hada da Zamfara dalibai 28, Taraba 95 sai Kebbi 50.

Hukumar ta bayyana za'a zana jarabawar kamar yanda aka tsara saidai tana kira da iyayen yara,makarantu da kuma kungiyoyi dasuyi kokari wajen magance matsalar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng