Yan bindiga sun gindaya ma gwamnati sharadin ajiye makamai da zaman lafiya a Zamfara

Yan bindiga sun gindaya ma gwamnati sharadin ajiye makamai da zaman lafiya a Zamfara

Biyo bayan wani umarni da gwamnan jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari ya bayar jami’an tsaro na cewa a duk inda aka hangi wani mutum dauke da bindiga, su bude masa wuta, su ma yan bindigan sun yi raddi.

Gwamna Yari ya bayyana haka ne a matsayin wani matakin magance yawan hare haren da ake samu a jihar, musamman tun bayan hallaka shugaban yan bindigan, Buharin Daji, inji majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Sharrin Almajiranci: An tsinci gawar wani Almajiri bayan an farke masa ciki a garin Katsina

Muryar Amurka ta ruwaito Yan bindigan sun bayyana cewar wannan mataki ba zai haifar da da mai ido ba, kamar yadda yaran Buharin daji suka bayyana. Yaran wadanda suka bayyana cewar su ne suka kai hari a kauyen Bawar Daji dake karamar hukumar Anka sun ce hakan ba zai samar da zaman lafiya ba.

Wakilin yaran Buharin Daji, mai suna Mohammed Bello ne ya bayyana haka, inda yace harin da suka kai kauyen Bawar Daji na ramuwar gayya ne, amma ya tabbatar ma majiyar Legit.ng cewa a shirye suke su yi sulhu da gwmanati.

Sai dai Bello ya gindaya sharadin sulhu, inda ya bukaci gwamnati ta daina kama yan uwansu, kuma ta da fatattakarsu daga gari. A nasa bangaren kuwa, gwamnan jihar Zamfara yace babu wani batun sulhu, inda yace sun sanya kafar wando daya da yan bindiga, tun da dai sulhun da aka yi a baya bai haifar da komai ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel