Ci da addnini: Pastocin Arewa sun ce in kun ji ana cewa Buhari zai musuluntar da Najeriya to siyasa ce

Ci da addnini: Pastocin Arewa sun ce in kun ji ana cewa Buhari zai musuluntar da Najeriya to siyasa ce

- Pastocin Arewa karkashin kungiyarasu ta Arewa Pastors Peace Initiative, Nigeria, APPIN, sun kaiwa Muhammadu Buhari ziraya

- Pastocin suka ce sun gane akwai baragurbi a cikinsu

wata kungiyar malaman kirista dake fafutukar tabbatar da zaman lafiya mai suna Arewa Pastors Peace Initiative, Nigeria, (APPIN) ta jadda aniyarta ta goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari, hakan dai ya fito ne daga bakin shugaban tawagar Bishop John Abu Richard, a yayin ziyararsu ga shugaban kasar a fadarsa dake Abuja jiya Alhamis.

Ci da addnini: Pastocin Arewa sun ce in kun ji ana cewa Buhari zai musuluntar da Najeriya to siyasa ce
Ci da addnini: Pastocin Arewa sun ce in kun ji ana cewa Buhari zai musuluntar da Najeriya to siyasa ce

A yau munzo ne don jaddada kudirinmu na cigaba da marawa wannan gwamnati baya, sakamakon hakikan cewar da mu kayi da cewa zabin Ubangiji ce” A jawabin Bishop John.

Pastor Abu Richard ya cigaba da cewa, “kungiyar ta sun a da mambobi har dubu arba’in da biyar a fadin Jahohi 19 na Arewa, wadanda duk babbar aniyarsa it ace wa’azi akan zaman lafiya da kuma kauracewa kalaman kiyayya da ka iya jawo tashin hankali."

Kuma sun hakikance kan cewa gwamnatin shugaba Buharin na kokakri wajen habaka tattalin arziki da dakile matsalar rashin tsaro da kuma farfado da harkar noma.”

KU KARANTA: Al-Mustapha ya bayyana yanda aka kashe Sani Abacha

Pastocin suka ce, “Hakika munyi murna a lokacin da shugaba Buharin ya warke daga matsananciyar rashin lafiyar da yayi. Sanan kuma suna fatan shugaban zai taimaka musu aiwatar da taron addu’ar da suke shirin gudanarwa ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu."

"Yunkurin da gwamnatinka take na dawo da zaman lafiya a duk fadin kasar nan abin a yaba ne, kuma mu ma zuwanmu nan na da nasaba da aniyarmu ta taimaka maka cimma wannan kudiri, ta hanyar dakile wasu daga Pastocin dake suke amfani da wuraren bauta domin furta maganganun da ka iya jawo rikici." Pastocin suka jaddada.

“Batun musultar da Najeriya da wasu mutane ke cewa zaka yi, kawai siyasa ce. Domin ´mun tabbata idan baka musuluntar da Najeriya a lokacin da kake soja kuma mataimakin ka shi ma musulmi; to lallai ba ba gaskiya a cikin wannan maganar.” A cewar Pastocin.

Daga karshe suka ce, wannan “matsalar ta rashin tsaro ba ta ware kirista ko musulmi mi, kowanne bari matsalar tayi musu illa. Kuma sunyi imanin gwamnati na kokarin magance matsalar, kana za suyi hadin gwuiwa da sauran kungiyoyin Pastocin dake gabashi da yammacin kasar nan don cimma burin wanzar da zaman lafiya da dakile kalaman kiyayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng