Hakurin da PDP ta bayar ba komai bane face yaudara – Kungiyar Musulunci

Hakurin da PDP ta bayar ba komai bane face yaudara – Kungiyar Musulunci

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci yan Najeriya da kada su yarda da hakurin da shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya bayar bisa kuskure da jam’iyyar tayi a baya, cewa hakan yaudara ne.

Kungiyar ta Musulunci tace hakurin bai cika ba domin basu bayyana ko jam’iyyar zata dawo da kudaden da ta sata ba ko kuma akasin haka.

A lokacin wani taron kasa a watan Maris, Mista Secondus ya bay an Najeriya hakuri kan kuskure da jam’iyyar ta tafka a lokacin da take kan mulki, inda yayi alkawarin cewa daga yanzu bazaar sake kama jam’iyyar da wani hali mara kyau ba.

Hakan ya janyo cece-kuce inda har jam’iyyar PDP ta buga sunaye da tayiwa lakabi da barayin gwamnati.

Hakurin da PDP ta bayar ba komai bane face yaudara – Kungiyar Musulunci
Hakurin da PDP ta bayar ba komai bane face yaudara – Kungiyar Musulunci

MURIC bayan taronta na CCT ta bayyana hakurin a matsayin yaudara da kuma mara amfani.

KU KARANTA KUMA: Zogala: Maganin dake kashe cutar daji ya kuma hana cutar siga

A wata sanarwa daga daraktanta, Ishaq Akintola, a ranar Alhamis kungiyar ta bayyana cewa aika-aikan da PDP tayi yafi gaban hakuri cewa jam’iyyar na bukatar wufanta cin hanci da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel