Rashin imani: Wani Uba ya kashe dansa ya arce

Rashin imani: Wani Uba ya kashe dansa ya arce

- Kisan yaron dai ya biyo bayan rigimar da sukai da mahaifin nasa

- Yan sanda na neman mahaifin wannan yaron, bayan da zakara ya bashi sa'a

Yanzu haka dai rundunar sanda reshen Jihar Enugu, na neman wani mahaifin yaro mai suna Kenneth Ajah, bayan da ya aike da dansa har lahira wai kawai don wata yar karamar hatsaniya ta barke a tsakaninsu.

Mahaifin yaron dai mai suna Onyenwe Offor Ajah, ya lakadawa dan nasa ne dukan kawo wuka hai sai da ya fita daga haiyacinsa.

Kakakin hukamar ta yan sanda reshen jihar ta Enugu, SP Ebere Amaraizu, ya tabbatar da faruwar hakan, in ya ce, a yanzu haka sun baza komarsu domin kamo wannan uban yaro, wanda tuni ya cika wandonsa da iska.

Rashin imani: Wani Uba ya kashe dansa ya arce
Rashin imani: Wani Uba ya kashe dansa ya arce

Wannan al’amari dai ya faru a ranar Larabar 28 ga watan maris a kauyen Ameke Enu na garin Oduma dake karamar hukumar Aninri ta Jihar Enugun.

KU KARANTA: Da lauje cikin naɗi: Batun sauyin lokutan zaɓe

Amaraizu yace, “Mahaifin yaron mai shekaru 38, ya kashe dan nasa ne bayan da wata rigima ta sarke a tsakaninu inda bayan ya gwada yar kwanji da shi ne, kana daga bisani sai kuma ya kwada masa wani abu a kansa, wanda nan take ya fita daga haiyacinsa, bayan an garzaya da shi asibiti ne ya ce ga garinku nan.”

Gawar wannan yaro dai yanzu haka na can a sashin ajiye gawawaki na babban asibitin dake yankin Awgu, yayin da su kuma yan sanda ke cigaba da neman wannan Uban yaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng