Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya

Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya

- In da ace yan Najeriya zasu gane kokarin da gwamnatin Buhari take da son bata maki dari bisa dari

- Mu rika godewa Allah da irin baiwar da yayi mana ta sanadiyyar zuwan gwamnatin shugaba Buhari domin ya kara mana.

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ja hankalin yan Najeriya da kada su zama tamkar kaji masu ci su goge baki. Martanin dai ya zo dai-dai lokacin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ke cigaba da fuskantar caccaka daga wurin mutane da dama.

Babban mai taimakawa Shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan, inda ya ce, kokarin da gwamantin Buharin keyi sai san barka musamman a fannin tattalin arziki, amma ya yarda akwai aiki ja a gaba.

Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya
Malam Garba Shehu

Garba Shehun dai ya bayyana haka ne a garin Abuja, inda yake cewa "yan Najeriya riba suka samu idan akai duba da irin sauye-sauyen da Muhammadu Buhari ya kawo a harkar tattalin arziki da ma sauran fannonin rayuwa da Buharin ke ta aiki tukuru domin cika alkawarin da yasa aka zabe shi a 2015.”

Ya kara da cewa, “Ko a shekarar da ta gabata sai da Najeriya ta samu lambar yabo daga Bankin Duniya inda sunanta ya koma na goma (10) a jadawalin sunayen kasashen da suke kokarin farfado da tattalin arzikinsu, wanda wannan wata babbar shaida ce dake nuni da irin namijin kokarin bullo da dabarun sake habaka tattalin arzikin Najeriya.” A cewar Garba Shehu.

A yau yan kasuwa daga ko’ina a fadin duniya na iya shigowa Najeriya kuma su karbi izinin zama (Visa) nan take ba tare da wata matsala ba, hakan kuwa daya ne daga cikin dalilan da suka sanya aka mayar da Najeriya mataki na 24 a jadawalin kasashen da ke da saukin aiwatar da sha’anin kasuwanci a duniya.

KU KARANTA: Zogale: Maganin dake kashe cutar daji ya kuma hana cutar siga

Ya kara ada cewa, gwamnati na kashe makudan kudade wajen aiwatar da sabbin manyan aiyuka fiye da gwamnatin da ta shude, duk kuwa da cewa a yanzu farashin danyan mai ya fadi, idan aka kwatanta shi da yadda ake siyarwa a shekarun 2011 zuwa 2014 da kimanin kashi hamsin cikin dari.

Shehu ya cigaba da cewa, jajircewar da shugaba Buhari yayi ce ta sanya har kasar nan ta fita daga cikin matsin tattalin arzikin da ta shiga, har kuma a yanzu aka samu gagarumar nasara a fannin akin noma, wanda a yanzu matsan kasar nan ke samar da kaso mafi yawa daga cikin abincin da muke ci.

Kana ya jaddada yadda gwamnatin tarayyar ta bullo da shirin bayar da rance ga dimbun matasa don shiga aikin noma, wanda hakan ya taimaka wajen sauya tunaninsu na jiran samun aikin office.

“Taki ya samu a farashi mai rahusa kuma matasa na ta tururuwa wurin shiga sana’ar noma don sun gano harka ce mai gwabi sosai.” Mataimakin shugaban ya fada.

Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya
Matasa na Noma

Malam Garba ya cigaba da cewa, “Wutar lantarki ta samu fiye da yadda take a shekarar 2015 lokacin da Buhari ya karbi mulki.”

Ana sa jawabin yayin taron da tsohon gwamnan Jihar Legos Bola Ahmed Tinubu ya shirya, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, cewa yayi, "Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zubu zunzurutun kudin da ya kai Naira biliyan dari biyar (N500b) a shirye-shiryen da zasu canza rayuwar al’umma, wanda wannan shi ne shirin kakkabe talauci mafi girma da wata kasa ta taba yi a yankin Sahara na nahiyar Africa."

Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya
Farfesa Yemi Osibanjo

Dukkuwa da cewa, farashin mai ya karye, da kusan kashi hamsin cikin dari sannan kuma hakar danyan Mai ya samu nakasu sakamakon aiyukan yan tsagerun Niger Delta, inda aka koma hako kasa da ganga dubu dari bakwai, maimakon miliyan biyu da ake iya hakowa a rana. Inji Farfesan.

A yau a tsare-tsaren da muka bullo da su, sunyi nasarar samarwa da matasa dubu dari buyu aikin karkashin tsarin Npower kuma da karin daukar wasu dubu dari ukun da aka sake zabowa.

Fiye da dalibai miliyan bakwai ne yanzu haka ake ciyar da su a Jihohi 22 na kasar nan, ga kuma kananan bashi da muka rabawa kusan mutane dubu dari uku tare kuma da karin wasu dubu dari ukun da ake bawa tallafin rage radadin talauci na hasafin Naira dubu biyar-biyar.

Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya
Npower

Osibanjo ya kuma cewa, “A yunkurin da suke na cika alkawuran da suka dauka yayin yakin neman zabe, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zuba makudan kudade wajen ganin an farfado da zirga-zirgar jirgin kasa, da ginin tituna da kuma wutar lantarki da sauran kayan more rayuwa."

"Shekarar 2014 da farashin Mai yake a $100 zuwa $114 ganga guda, kudaden da aka sakarwa ma’aikatar makamashi da ta aiyuka da ta kuma gidaje, a lokacin suna maikatu daban-daban jimillarsu shi ne naira biliyan casa’in da tara (N99 billion), yayinda aka bawa ma’aikatar aikin gona biliyan goma sha biyar (N15b). wannan sune gaskiyar kudaden da aka basu, ba wanda aka ce za’a basu ba a cikin kundin kasafi ba. A cewar Osinbajon."

Kana ya ce domin bambance aya da tsakuwa kuwa, duk da cewa an hade ma’aikatar makamashi da aiyuka da gidaje wuri guda, "A shekarar 2017 an basu zunzurutun kudin da yakai, Naira biliyan dari hudu da goma sha biyar (N415b) da kuma biliyan tamanin (N80b) ga ma’aikatar sufuri, da biliyan sittin da biyar ga ma’aikatar gona, wanda idan ka hada lissafin ya kai wuri na gugar wuri har Naira biliyan 560.

Kar da ku zama kamar kaji masu ci su goge baki mana, a martanin fadar shugabn kasa ga ƴan Najeriya
Jirgin kasa

"Dukkuwa da cewa muna fuskantar kalubalen rashin kudi, domin idan aka kwatanta zaka ga kusan kudin da muke samu yanzu kamar rabin wanda suka samu ne a shekarar 2014." A cewar mataimakin shugaban kasar.

Sannan ya kuma ce, “muna fatan ba za’a samu wadanda zasu cudanya wannan rahoton namu da karya ba, domin akwai abubuwa da yawa da zamu cigaba da aiwatarwa domin samar da cigaba ga rayuwar yan Najeriya.

Ya zama tilas mu dakatar da dabi’ar son rai da suka mara tushe balle makama gami da rashin godiyar abinda yake hannun mu sakamakon hanken na hannun wani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel