Yadda Gwamnatin Buhari ta ke bunkasa harkar noma a Najeriya
- Bisa dukkan alamu manoma za su ji dadin aikin gona wannan shekara
- Gwamnati za ta taimaka wajen samar da isasshen takin zamani a kasar
- A bara an saida takin zamani na NPK 20-10-10 ne a kan farashi N5, 500
Wani tsari da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo na inganta takin zamani watau PFI na shirin samar da akalla metric tan har miliyan guda na takin zamani domin manoma a wannan shekarar.
Thomas Etuh wanda shi ne Shugaban Kungiyar FEPSAN na masu hada takin zamani a kasar ya bayyana cewa za nunka yawan takin NPK 20-10-10 da aka hada a bara a wannan shekarar wanda ake saidawa manoman kasar a N5, 500.
KU KARANTA: Gwamnan CBN ya fadawa Buhari don tuwon gobe ake wanke tukunya
A bara dai an samar da buhunan taki na zamani tan 500, 000 inda a bana ake sa rai a samu akalla tan 1, 000, 000. FEPSAN ta hada kai da wasu bankunan kasar wajen ganin an samu isasshen takin da za ayi noma da shi a wannan shekarar.
Wani babban Ma’aikacin Union Bank Bona Okhaimo ya tabbatar da cewa da gaske su ke yi wajen habaka harkar noma a kasar don haka ne aka ba masu harkar taki aron kudi domin su yi kasuwancin su da kyau ba tare da samun matsala ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng