Nigerian news All categories All tags
Uba ya cika wandonsa da iska bayan ya kashe ɗansa sakamakon wata yar saɓani da suka samu

Uba ya cika wandonsa da iska bayan ya kashe ɗansa sakamakon wata yar saɓani da suka samu

Rundunar Yansandan jihar Enugu ta shiga neman wani mutumi mai suna Onyenwe Offor ruwa a jallo bayan zarginsa da ake yi da hallaka dan cikinsa a jihar Enugu, inji rahoton Daily Nigerian.

Kaakakin rundunar, Ebere Amaraizu ne ta tabbatar da hakan, inda tace lamarin ya faru ne a ranar Laraba 28 ga watan Maris, a kauyen Ameke Enu dake garin Oduma a cikin karamar hukumar Aninri, inda Offor ya kashe dansa mai suna Kenneth Ajah mai shekaru 37.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bada umarnin fitar da kudi naira biliyan 360 don siyan makamai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa yaron da mahaifinsa sun samu rashin jituwa ne a tsakaninsu tun a kasuwar Orie Oduma, wanda hakan yayi sanadiyyar cacar baki a tsakaninsu, har suka dambace, daga nan kuma mahaifin ya dauki wani karfe ya danka ma yaron a kai, nan take ya fadi matacce.

Duk da an garzaya da shi asibiti da gaggawa, a can ma likitoci sun tabbatar da mutuwar yaron, inda a yanzu haka an jibge gawarsa a dakin gawa na babban asibitin gwamnati dake garin Awgu, kuma tuni Yansanda suka baza komarsu da cafke mahaifin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel