Wata uwa ta jibgi diyar ta har saida ta mutu saboda tana tara samari

Wata uwa ta jibgi diyar ta har saida ta mutu saboda tana tara samari

Yan sanda a Macheke dake kasar Zimbabwe sun kama wata mata bisa zarginta da kasha diyar ta budurwa; mai shekaru 16, saboda tana tara samari.

Matar, Stella Mwale; mai shekaru 38, na bawa jami’an ‘yan sanda muhimman bayanai dangane da mutuwar diyar ta, Hilda Chikumba, bayan dukan da ta lakada mata.

Kakakin hukumar ‘yan sanda, Tendai Mwanza, na ofishin Mashonaland dake yankin gabashin kasar Zimbabwe, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Wata uwa ta jibgi diyar ta har saida ta mutu saboda tana tara samari

Wata uwa ta jibgi diyar ta har saida ta mutu saboda tana tara samari

Na tabbatar da mutuwar wata matashiya, da mahaifiyar ta lakadawa duka saboda yawan samari. Ina mai rokon mutane das u guji yin hukunci yayin da suke cikin fushi. Yana da muhimmanci mutane su bari har sai sun samu natsuwa kafin zartar da kowanne irin hukunci,” a cewar kakakin.

Rahoton ‘yan sanda y ace, a ranar 30 ga watan Maris, Mwale ta ziyarci diyar ta dake zaune da ‘yar uwar ta a Macheke. Mahaifiyar ta shawarci diyarta Hilda da ta mayar da hankali kan karatunta, ta daina biyewa samari.

DUBA WANNAN: Gwamna Bello ya halarci taro a fadar shugaban kasa cikin sandar guragu

Saidai diyar ta amsawa mahaifiyar ta cikin gatsali cewar, ta kai munzali a saboda haka ta kyaleta tayi duk yadda take so da rayuwar ta. Amsar da yarinyar ta bayar bata yiwa mahaifiyar ta dadi ba, hakan ya saka ta fusata har ta rufe tad a dukan da ya zama silar mutuwar ta.

Hukumar ;yan sandan t ace zata gurfanar da Mwale gaban kotu bisa tuhumar tad a aikata laifin kisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel