Kasar Isra'ila na da ikon kasancewa a inda take ba tare da tsangwama ba - Yarima Mohammed bin Salman
Yarima mai jiran gado masarautar Saudiyya mai suna Mohammed bin Salman ya nuna goyon bayan sa ga me da cigaban zaman kasar Isra'ila a bagiren da take yanzu na tsakanin kasashen Larabawa a gabas ta tsakiya ba tare da tsangwama ko kyara ba.
Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana hakan ne a yayin da yake fira da wata jaridar kasar Amurka mai suna The Atlantic Magazine yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar a makon da ya gabata.
KU KARANTA: Yadda zan kawo karshen rikicin Najeriya - Sule Lamido
Legit.ng ta samu cewa shi dai Yariman mai shekaru 32 a duniya ya kuma bayyana cewa shi yayi ammanar Yahudawa a duk inda suke suna da 'yancin zama ba tare da tsangwama ba kamar yadda kuma yake ganin suma 'yan Falasdinawa suna da 'yancin zama a inda suke.
A wani labarin kuma, Yayin da kasar Saudiyya ke ta dada kara shiga cikin cakwakiyar rikicin addini sakamakon kokarin kawo sauye-sauye a kasar da Yarima Mohammed bin Salman ke yi, ya bayyana cewa shi a kasar sa yanzu babu sauran banbanci a tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunni.
Yariman yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da wata jaridar Atlantic a nahiyar turai inda yake ziyarar aiki tun satin da ya shude.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng