Wani tsohon ‘Dan Majalisa ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi

Wani tsohon ‘Dan Majalisa ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi

- Wani tsohon ‘Dan Majalisa ya fara harin kujerar Marigayi Sanata Ali Wakili

- Kwanakin baya ne Sanata Ali Wakili ya zare jiki ya mutu ana zaune kwatsam

- Gebi yace kamar yadda Sanatan bai san zai mutu ba babu wanda ya san 2019

Mu na da labari cewa wani tsohon ‘Dan Majalisar wakilan Tarayya na Jihar Bauchi ya fito takarar kujerar Sanatan Kudancin Bauchi bayan rasuwar Sanata Ali Wakili wanda ya ke kan kujerar a da.

Wani tsohon ‘Dan Majalisa ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi
Aliyu Gebi ya fito takarar Sanatan Bauchi ta Kudu

Aliyu Ibrahim Gebi wanda ya taba zuwa Majalisa a karkashin Jam’iyyar CPC a 2011 yace za a buga da shi wajen takarar kujeran Sanatan Kudancin Bauchi a zaben da za ayi. Ali Gebi yace babu wanda ya san gobe sai Allah.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta fitar da sunayen Waliyyan Najeriya - Sani

Yanzu dai Gebi yana cikin masu ba Ministan harkokin cikin gida watau Janar Abdulrahman Dambazau (Mai ritaya) shawara. Akwai wani mai ba tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yugudu shawara da ya fito takarar wannan kujera.

A lokacin da yake yi wa manema labarai bayani, tsohon ‘Dan Majalisan Tarayyar ya koka da rikicin da ake yi tsakanin Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya Yakubu Dogara da kuma Gwamnan Jihar Bauchi MA Abubakar ya nemi a hada kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng