Nigerian news All categories All tags
'Yar gagara: Wata yarinya mai shekaru 15 ta gudu daga gida saboda an hana ta halin karya

'Yar gagara: Wata yarinya mai shekaru 15 ta gudu daga gida saboda an hana ta halin karya

Wata yarinya mai shekaru 15, Oluwakemi Abayomi, ta gudu daga gida bayan mahafiyarta, Mariyam Lebi ta gargadeta akan biyewa samari.

Oluwakemi ‘yar aji shida ce a makarantar frimari kuma ita ce diya ta farko a wurin mahaifiyarta, wadda ke da yara shida kuma ma'aikaciyar tsaftace muhalli ne a wata makarantar gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifiyarta ta kasance bata tare da baban yarinyar, ta bayyana cewa diyar ta bata dawo gida ba tun ranar Lahadi da misalin karfe 1 na rana da ta bar gida kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

'Yar gagara: Wata yarinya mai shekaru 15 ta gudu daga gida saboda an hana ta halin karya

'Yar gagara: Wata yarinya mai shekaru 15 ta gudu daga gida saboda an hana ta halin karya

Mahaifiyar Oluwakemi ta cigaba da cewa " Diyar tawa tana zama ne tare da kakarta a kusa da gabar rafin Lekki ni kuma ina zaune ne a Itedo wanda dan tafiya ne kadan daga inda suke zaune. Duk da cewa tana zaune da kakarta tun tana yar shekatu biyar, ni nake daukan nauyin hidimominta don mun rabu da mahaifinta tun tana jinjira".

KU KARANTA: Komai nisan jifa: An kama dukkan 'yan dabar Dino Melaye da suka tsere daga hannun 'yan sanda, ku kalli fuskokinsu

Na samu labarin irin halin da ta fara na biyewa samari hsksn yasa na ce ta kwaso kayanta ta dwo wajena. Nayi mata gargadi kuma na ce mata zan dauke ta daga unguwar nan bayan ta rubuta jarabawar shiga makarantar Sakandire.

"Ta tafi gidan kakarta don ta kwaso kayanta amma bamu sake ganin ta ba. Daga baya wani mai kabu-kabu da na sani ya fada min cewa ya dauke ta zuwa tasha inda ta shiga motar zuwa Ajah."

Ms Lebi ta shiga damuwa ne sosai bayan kakar yarinyar ta kira ta domin tambaya ko Oluwakemi ta iso gida, tayi cigiya da tambaya cikin kawayen Oluwakemi amma babu wanda ya san inda ta tafi.

Daga baya na samu labarin cewa ranar Laraba da ya gabata wani mutum ya zo neman ta a makaranta inda ya rubuta lambar tarho ya mika mata amma babu wanda ya san mutumin. Bisa ga dukkan alamu ta fara bin maza ne shiyasa nayi niyyar canja mata wurin zama amma banyi tsaminin zata gudu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel