Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya ta tura dakarun soji na musamman jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya ta tura dakarun soji na musamman jihar Zamfara

Hukumar sojin saman Najeriya ta tura dakarun soji na musamman Gusau, babban birnin jihar Zamfara a yau Talata, 3 ga watan Afrilu, 2018.

Hukumar ta dau wannan mataki ne bayan kisan rashin imanin da wasu yan bindiga suka kai jihar Zamfara inda suka hallaka jama’a ba babba ba yaro.

Kakakin hukumar NAF, Olatokunbo Adesanya, ya bayyana wannan labari ne a wani jawabi da ya saki da yammacin yau Talata.

Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya ta tura dakarun soji na musamman jihar Zamfara
Yanzu-yanzu: Hukumar sojin Najeriya ta tura dakarun soji na musamman jihar Zamfara

Jawabin yace: “Bisa ga harin da aka kai garin Bawar Daji, da ke karamar hukumar Anka na jihar Zamfara inda aka yi asaran rayuka, babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya bada umurnin tura jami’an sojin saman na musamman garin Gusau domin kawo karshen wannan aika-aika.

Jami’’an sojin tare da wasu dakarun zasuyi aiki daga Gusau inda zasu karawa jami’an Operation SHARAN DAJI karfin guiwa.

Kwamandan ayyukan runduna na musamman, Air Vice Marshal Ismaila Kaita, ya alanta a jawbinsa cewa za’a tura jami’an kauyukan jihar Zamfara ne inda za su taimaka wajen ayyukan cikin gida.

Ya kara da cewa yana kyautatat zaton jami’an sojin za’a nua kwarewa wajen aikinsu da kuma kare hakkin bil adama.”

Ranan Alhamis da ya gabata, yan baranda sun hallaka jama'a a jihar Zamfara wanda ya sanya gwamnati ta bada umurnin kashe duk wanda aka gani da bindiga a jihar Zamfara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng