Rundunar yan sanda sun gano makamai 119
- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Jigawa sun gano manyan makamai 116, da harsasai 65, sai akwatin harsashi 6
- Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Bala Sanci, yace aikin ya kasance umarnin da shugaban ‘Yan Sandan na kasa Ibrahim Idris a kan yaki da masu amfani da makamai bada izinin doka ba
- Yace yawancin makaman an samesu ne ta hannun masu su wadanda suka bayar dasu ga hukumar ‘Yan Sandan cikin lalama
Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Jigawa sun gano manyan makamai 116, da harsasai 65, sai akwatin harsashi 6.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Bala Sanci, yace aikin ya kasance umarnin da shugaban ‘Yan Sandan na kasa Ibrahim Idris a kan yaki da masu amfani da makamai bada izinin doka ba.
An samu bindigogi 104 kirar baushe, sai bindigogin kugu na hausa guda biyar, sai AK-47 guda uku, sai manyan bindigogi guda uku na hausa, sai AK 56 guda biyu, bindigar kugu ta bature guda daya, sannan sai harba ruga guda daya.
KU KARANTA KUMA: Ben Bruce ya caccaki Garba Shehu kan furuci da yayi
Mista Sanci yace yawancin makaman an samesu ne ta hannun masu su wadanda suka bayar dasu ga hukumar ‘Yan Sandan cikin lalama.
Daga karshe yayi kira ga sauran wadanda keda makaman da su bayar dasu kafin a kamasu dashi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng