Kaduna: Baza mu yafewa duk wani dan kudancin Kaduna daya zabi El-Rufai ba - Inji tsohon kwamishina Mikaiah Tokwak
- Wani tsohon kwamishinan jihar Kaduna kuma daya daga cikin manyan jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Mista Mikaiah Tokwak, ya bayyana cewa, Gwamna Nasir El-Rufai ya taba gaya masa cewa ba dole sai da kuri'un mutanen kudancin Kaduna zai lashe zabe ba a shekarar 2019
Wani tsohon kwamishinan jihar Kaduna kuma daya daga cikin manyan jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Mista Mikaiah Tokwak, ya bayyana cewa, Gwamna Nasir El-Rufai ya taba gaya masa cewa ba dole sai da kuri'un mutanen kudancin Kaduna zai lashe zabe ba a shekarar 2019.
DUBA WANNAN: Barayin Gwamnati: Akwai makirci a cikin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na barayin dukiyar kasa - Ferdinand Orbih
Tokwak, ya ce baza su yafe wa duk wani dan kudancin Kaduna daya dangwalawa gwamnan ba a zaben shekara mai zuwa ta 2019. Tsohon kwamishinan wanda yayi magana da kungiyar matasa da kuma mata a karamar hukumar Jaba dake yankin kudancin Kaduna, a wani taro da suka kirashi da suna, "Wayarwa da matasa da kuma mata kai akan harkar siyasa".
Ya ce: "Kuje ku gaya wa gwamna Nasir El-Rufai cewar ni, Mikaiah Tokwak nace baza mu yafewa duk wani dan kudancin Kaduna daya zabe shi ba."
Tokwak, ya ce El-Rufai ya samu kujerar gwamnan Kaduna ne ta dalilin zaben shi da mutanen kudancin Kaduna suka yi, domin kuwa mutanen sa basu zabe shi ba. Ya kara da bayyana cewar mutanen yankin kudancin na Kaduna sun bashi kashi 75 cikin dari na kuri'ar su.
"Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa, Sanata Hunkuyi shine ya kira mu domin mu gana dashi, inda yake cewa muna da kashi 30 cikin dari a jihar Kaduna amma kuma mune muke rike da manyan ma'aikatu na jihar nan."
El-Rufai ya taba cewa bai bukatar kuri'un mutanen yankin kudancin Kaduna ko daya domin lashe zaben shekarar 2019, to tunda har gwamnan da kanshi ya fada cewar baya bukata menene zai saka ku zabe shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng