Jerin barayin kasa: Sharrin Gwamnatin APC ne Inji Sanata Stella Oduah
- Gwamnatin Buhari ta fitar da wani sunaye na wadanda su ka saci kudi a kasar
- Oduah wanda tayi Minista lokacin Shugaba Jonathan tana sahun farko a jerin
- Sanatan PDP a kasar a yanzu dai ta musanya cewa tana cikin barayin Najeriya
Kun samu labari cewa kwanan nan ne Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cika umarnin Kotu da aka bukaci ta bayyana sunayen wadanda su ka saci kudin kasar nan. Daga ciki akwai wata tsohuwar Ministan kasar Stella Oduah.
Stella Oduah wanda ta rike Ministan sufurin jirgin sama a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta musanya cewa tana cikin wadanda su ka sace dukiyar Najeriya kamar yadda Gwamnatin APC ta bayyana.
KU KARANTA: An fadawa Dattawan Arewa cewa Buhari bai da na-biyu
Oduah tayi amfani da shafin ta na sadarwa na Tuwita ta nuna cewa karya ce kurum ta Gwamnatin Buhari wanda a baya ta zarge ta da cewa an samu makudan kudi da su ka kai kusan Naira Biliyan 2 a asusun wata mai-aikin ta.
A jerin wasu barayin da Ministan yada labarai Lai Mohammed ya saki kwanan nan, sunan Sanata Stella Oduah ta Anambra tana gaba-gaba inda aka bayyana cewa ta saci Biliyan 9.8 wajen ta da kuma wasu gidaje masu ‘dan karen tsada.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng