Ba laifi don mutum ya kare kanshi a lokacin da ake shirin cutar dashi - Shawarar da fadar shugaban kasa ta bawa 'yan Najeriya
- Mataimakin shugaban kasa na musamman a bangaren yada labarai, Mal. Garba Shehu, yace babu laifi idan mutum ya kare kanshi lokacin da 'yan ta'adda suka kai masa hari, amma kuma dole ayi hakan bisa yanda doka ta tsara
Mataimakin shugaban kasa na musamman a bangaren yada labarai, Mal. Garba Shehu, yace babu laifi idan mutum ya kare kanshi lokacin da 'yan ta'adda suka kai masa hari, amma kuma dole ayi hakan bisa yanda doka ta tsara.
DUBA WANNAN:
Hakan ya biyo bayan wata sanarwa da tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma (Rtd), ya fitar, inda yake cewa kowanne dan Najeriya yayi kokarin kare kanshi daga irin tashin hankulan dake faruwa a wasu sassa na kasar nan.
Mal. Shehu wanda ya yi bayani a gidan talabijin na Channels, ya jaddadawa mutane cewa dole ya kasance duk wanda zai kare kanshi to yayi hakan bisa yanda dokja ta tanada.
"Babu wani laifi dan kun kare kanku daga sharrin 'yan ta'adda muddin zaku yi hakan bisa yanda doka ta tanada, inji shi."
A ranar 24 ga watan Maris dinnan ne Janar T.Y. Danjuma, ya zargi hukumar tsaro ta soja akan cewar da hadin bakin su ake aikata duk wata ta'asa a kasar nan. A cewar tsohon ministan tsaron, a lokacin da yaje wani taro a jami'ar jihar Taraba, inda yake cewa tsaro a jihar taraba yana fuskantar mummunar barazana. Akwai kokarin daya kamata muyi shine muga mun kawar da kabilanci a jihar nan.
Mal. Garba Shehu ya ce ya tabbata cewar shugaba Buhari yaji abinda Janar Danjuma yace, kuma yana kokari wurin ganin yayi amfani da shawarar tashi domin ganin an kawo cigaba ga kasar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng