Tolu Ogunlesi yayi kaca-kaca da masu yi Naomi Campbell shaidar banza
Wani daga cikin Hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna Tolu Ogunlesi yayi kaca-kaca da Jama'a a dalilin surutun da ake tayi game da hoton da Shugaban kasa ya dauka da wata shararriyar Tauraruwa Naomi Campbell.
Kwanan nan ne Shugaban kasa Buhari ya je Garin Legas inda ya kaddamar da wasu ayyuka. A nan dai Naomi Campbell wanda tayi fice a Kasar Birtaniya ta samu damar ganawa da Shugaban kasar inda har su kayi hotuna aka kuma baza a Duniya.
Wasu sun sa alamar tambaya bayan da Naomi Campbell tace Shugaba Buhari ne ya gayyace ta zuwa wurin taron. Ko da yake dai tayi maza ta sake magana bayan wani Hadimin Shugaban kasa mai suna Bashir Ahmad yace babu wanda ya gayyace ta.
KU KARANTA: Jam'iyyar PDP na neman tonawa Shugaba Buhari asiri
Tolu Ogunlesi ya nuna cewa babu komai don Shugaban kasa Buhari ya gana da Campbell wanda gumin ta ta ke ci. Ogunlesi yace har Marigayi Nelson Mandela na Afrika ta Kudu ya taba rungumar Campbell ya yabe ta don haka masu babatu ma dabbobi ne.
Sai dai bayan Ogunlesi ya zagi masu yi wa Naomi Campbell shaidar banza da sunan dabbobi yayi maza ya bada hakuri a shafin Tuwita na wannan subul-da-baka da yayi ya kuma nuna cewa hakan ba zai sake faruwa ba don kuwa ya dauki darasi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng