Cika alkawari: Babban malamin addini a Najeriya ya caccaki shugaba Buhari

Cika alkawari: Babban malamin addini a Najeriya ya caccaki shugaba Buhari

Wani babban malamin addinin Kirista a Najeriya kuma shugaban darikar Katolika na shiyyar Sokoto Bishof Matthew Hassan Kuka ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta tabbatar da cika alkawurran da ya daukar wa 'yan Najeriya lokacin yakin neman zabe.

Haka ma dai Bishof din ya kuma roki sauran 'yan Najeriya musamman ma masu fada a ji da su yi anfani da damar su wajen samarwa kasar tabbataccen zaman lafiya tare kuma gudun duniya da son tara dukiya.

Cika alkawari: Babban malamin addini a Najeriya ya caccaki shugaba Buhari
Cika alkawari: Babban malamin addini a Najeriya ya caccaki shugaba Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda tsaffin gwamnonin PDP suka ba Buhari Naira miliyan 500 - Bafarawa

Legit.ng ta samu cewa Bishop Kukah din yayi wannan kiran ne a cikin wani sakon bukukuwan Esta da ya fitar domin taya sauran mabiya addinin na kirista murnar zagayowar ranar.

A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya a ranar Asabar din da ta gabata ta fitar da sanarwa tana mai maida martani ga tsohon babban jami'in rundunar sojojin Najeriya kuma tsohon ministan tsaron kasar nan watau Laftanal Janar Theophilus Yakubu Danjuma (Mai ritaya) da yayi a satin da ya shude.

Idan dai ba'a manta ba Laftanal Janar Theophilus Yakubu Danjuma (Mai ritaya) a baya ya yi kira ga dukkan al'ummar kasar nan da su tashi tsaye wajen kare kansu da kansu idan har aka zo kawo masu hari domin a cewar sa jami'an tsaron Najeriya sun gaza ta wannan fannin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng