Masoya sun kashe kansu a Ingila rungume da juna, inda suka shiga gaban jirgin kasa

Masoya sun kashe kansu a Ingila rungume da juna, inda suka shiga gaban jirgin kasa

- Abin tausayin ya faru ne a Doncaster a Ingila

- Masoyan sun yi tsalle sun shiga gaban jirgin ya niqe su

- An rufe tashar domin bincike

Masoya sun kashe kansu a Ingila rungume da juna, inda suka shiga gaban jirgin kasa
Masoya sun kashe kansu a Ingila rungume da juna, inda suka shiga gaban jirgin kasa

A labari mai ban tausayi, wasu masoya guda biyu, matasa, mace da namiji, sunyi kundumbalar halaka kansu ta hanyar shiga gaban jirgin kasa inda yake gudu domin ya nike su, ya kuwa markade sun har lahira a talatar nan da ta wuce.

Ba'a dai san ko su waye ba, ko ma kuma me ya kaisu wannan mummunar aika-aika, inda ake sa rai dai matsanancin halin rayuwa ko tabin hankali ne ya same su suka gwammace baccin da ba tashi har abada.

DUBA WANNAN: Wasu kwayoyin ya kamata a halarta su

Kashe kai dai, wani abu ne da ke zame wa duniya annoba, inda akan sami mutane da yawa da ko dai sun kashe kansu ko kuma sun so yin hakan sun kasa.

Yawanci tsangwama, talauci, rashin farin ciki ko tabin hankali kan kai mutane kashe kansu da kansu, su bar mutane da tausayi da alhini.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: