Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta fara nesanta kanta daga wahabiyanci, Yarima mai jiran gado yace Turawa suka sanya su yada ta a duniya

Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta fara nesanta kanta daga wahabiyanci, Yarima mai jiran gado yace Turawa suka sanya su yada ta a duniya

- Tun bayan hawansa karagar Yarima mai jiran gado, MBS ya fara kawo manyan sauye sauye ga kasarsa

- Yace ya fahimci cewa ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da ake a duniiya da laifin kasar sa, ya kuma sha alwashin kakkabe wannan daga duniya

- Ya soke hukumar Hizba ta kasarsa ya kuma bar mata suyi tuki, ko su je gidan kida, silima, dama kuma ra'ayin ko su sanya ko su cire hijabi

Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta fara nesanta kanta daga wahabiyanci, Yarima mai jiran gado yace Turawa suka sanya su yada ta a duniya
Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta fara nesanta kanta daga wahabiyanci, Yarima mai jiran gado yace Turawa suka sanya su yada ta a duniya

Yarima mai jiran gado a Saudiyya, saurayi dan shekaru 33, a sabuwar baram-barama, cikin manyan sauye-sauye da yake kawo wa kasar sa cikin 'yan watannin nan, ya sake barota, inda yace gaba daya ma akidar wahabiyanci da kasarsa ta yada shekaru kusan 40 ga kasashen musulmin duniya, ba da son kansu bane.

A cewarsa dai, tsoron kasar Rasha ta wancan lokacin, watau USSR mai yada akidar Kwaminisanci da gurguzu, wanda yake tafe da ilhadi na kin yarda da samuwar alloli, yasa Turawan yamma na jari hujja suka ingiza Saudiyyar yada tata zazzafar akidar ta son addini dama kara imani.

Sai dai hakan yazo musu a daidai, domin kuma suma suna tsoron kasar Iran, wadda a daidai wannan lokaci ta fara yada Shi'anci da juyin -juya hali da ma nasu irin zafin ra'ayin domin a kafa daula karkashin Ahlul baiti masu bakin rawani, wanda hakan ke nufin a kori Al-Saud daga mulkin haramai na Makka da Madina.

Don haka nema, Saudiyyar ta zage damtse wajen bude markaz-markaz, cibiyoyi, masallatai, Islamiyyoyi, da ma tsangayoyi na ISlamic Foundation a kasashe don yada nata ra'ayin kan addini karkashin fahimtar Sheikh Abdulwahab, watau Wahabiyanci ko Salaf, wanda a Najeriya aka fi sani da Izala ko Ahlussunna.

DUBA WANNAN: Kwayar da tafi kowacce illa a jikin bil-Adama

Ga abin da yake fadi ga jaridar Washington Post a ziyararsa a Amurka: “Kawayen Saudiyya na yammacin duniya ne suka Tirsasa masarautarmu yada wahabiyanci, gina makarantun Islamiyya da masallatai, a tsakiyar karni na 20 don hana tarayyar Soviet samun gindin zama a kasashen Musulmai.

Makudan bilyoyin dalolin da muka zuba don yada wannan akidar sun fito ne daga kungiyoyi, hukumomi da ma’aikatu masu zaman kansu da ke kasarmu. Sarakunan Saudiyya da suka wuce sun aikata babban kuskure. Yanzu lokaci ne ya kamata a ce mun gyara kura-kuranmu”.

Kungiyoyin ta'addanci masu aiki da sunan addinin Islama dai, kamar su Alqaida ta Osama bin Laden, ISIS, Boko Haram, Lashkar e taiba, Taliban, Al-Shabab da dai sauransu duk daga irin wannan karatu suka kwashi mummunar akidarsu, kamar yadda binciken sashen Addinai na CIA ta Amurka ya wallafa kan yaki da ta'addanci a fadin duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar kuna ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel