Kisan Zamfara: Cikin kuka, Sarkin Anka ya nemi taimakon majalisar dinkin duniya, tarayyar Afrika

Kisan Zamfara: Cikin kuka, Sarkin Anka ya nemi taimakon majalisar dinkin duniya, tarayyar Afrika

A cikin wani yanayi mai cike da ban tausayi mai kama da shasshekar kuka, Sarkin masarautar Anka ta jihar Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da tarayyar turai da su kawo wa jama'ar sa agajin gaggawa.

Sarkin ya ce yanzu kam dai ya zama wajibi ya nemi taimakon al'ummar duniya don ganin an kawo karshen kisan kiyashin da yan bindiga da ake kyautata zaton barayin shanu ne suke yi wa jama'ar sa.

Kisan Zamfara: Cikin kuka, Sarkin Anka ya nemi taimakon majalisar dinkin duniya, tarayyar Afrika
Kisan Zamfara: Cikin kuka, Sarkin Anka ya nemi taimakon majalisar dinkin duniya, tarayyar Afrika

KU KARANTA: Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun yi barna a Kaduna

Legit.ng Alhaji Attahiru yayi wannan kiran ne a yayin wata huduba da yayi a masallacin juma'ar garin a ranar Juma'ar da ta gabata lokaci guda kuma da ya bukaci gwamnati ta kafa wani kwamitin binciken lamarin.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar Alhaji Abdulaziz Yari ya bayar da umurni ga jami'an tsaron kasar musamman ma wadanda suke a jihar sa inda ake ta kashe-kashe cewar su harbe dukkan wani farar hula da suka gani rike da makami.

Haka ma Gwamnan ya kara da cewa su ma dukkan masu garkuwa da mutane ko kuma masu bayar da wurin boye su su ma a kashe su da agan su ba tare da wata-wata ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng