Tuban mazuru Jam’iyyar PDP tayi saboda zaben 2019 – Inji Shugaba Buhari
- Buhari ya maidawa Jam’iyyar adawa PDP martani na ba ‘Yan Najeriya hakuri
- Shugaban kasar yace Gwamnatin sa tana cin bashi ne domin tayi wa jama’a aiki
- Buhari yace kawai ‘Yan PDP su maido kudin da su ka sace ba su nemi gafara ba
Idan ba ku manta ba Jam’iyyar adawa ta PDP ta bakin Shugaban ta Uche Secondus, ta bada hakurin abin da ya faru a lokacin da tayi shekaru 16 tana mulkin kasar nan. Dazu Fadar Shugaban kasa ta maidawa Jam’iyyar martani game da maganar.
Dazu nan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bakin mai magana da yawun sa watau Garba Shehu ya nemi ‘Yan Najeriya su guji biyewa zakin bakin PDP inda yace yunkurin dawowa mulki ne ya jawo Jan’iyyar ta ke ba mutane hakuri.
KU KARANTA: 'Yan Najeriya su yafe mana zunuban mu Inji PDP
Shugaban kasar yace Jam’iyyar ta PDP ba ta ma fito ta furta cewa ita ta rusa tattalin arzikin kasar ba, sannan kuma ta dauki yaki da satar da ake yi a matsayin yakin da ake yi da ‘ya ‘yan ta don haka hakurin da ta bada bai kai cikin zuciya ba.
Garba Shehu yace ba hakuri kurum PDP za ta bada ba, ya zama dole ta maido abin da ta sace, sannan sai tace ta tuba. Buhari yace Gwamnatin sa na karbo bashi ne domin yi wa kasa aiki ba sacewa ba sannan kuma ya nuna kokari wajen harkar tsaro.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng