Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati lokacin mulkin PDP
Gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen wadanda suka sace kudaden al'umma da aka damka masu amana a lokacin gwamnatin PDP. Gwamnatin, ta bakin ministan yada labarai, Lai Mohammed, ta saki sunayen mutanen ne a matsayin raddi ga jam'iyyar PDP na cewar ta saki sunan wadanda suka saci dukiyar kasa lokacin mulkinsu idan suna da shaida.
Da yake bayyana sunayen, Lai Mohammed, ya ce, "jam'iyyar PDP ta kalubalence mu da mu bayyana sunayen jami'an gwamnati da suka saci kudin al'umma lokacin mulkinsu. Sun musanta cewar an tafka almundahana a lokacin mulkinsu duk da sun san an tafkar muguwar barna a lokacin mulkinsu. Hakan ya nuna cewar har yanzu jam'iyyar PDP bata yi nadamar abinda ta aikata ba."
Duba jerin sunayen mutanen da Ministan ya bayyana da adadin kudin da suka sata, wadanda kuma tuni gwamnatin tarayya ta gurfanar da su;
1) Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus: Ya karbi miliyan 200 ranar 19 ga watan Fabrairun 2015 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA).
2) Tsohon sakataren kudin jam'iyyar PDP: A ranar 24 ga watan Oktoba, 2014, ya karbi miliyan N600m daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa a kan harkar tsaro.
KU KARANTA: Shugabanin da suka mulki Najeriya tun 1999
3) Tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Olisah Metuh: Ana tuhumar sa da karbar biliyan N1.4bn daga ofishin tsohon NSA.
4) Dakta Raymond Dokpesi: Shugaban kamfanin DAAR; mai gidan talabijin na AIT da gidan Radiyon Ray Power. Ana tuhumar sa da karbar biliyan 2.1 daga ofishin tsohon NSA.
5) Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara, Dudafa Waripamo-Owei: An gurfanar da shi bisa boye kudi miliyan N830m a asusu daban-daban.
6) Robert Azibaola: Dan uwa ga Jonathan: An gurfanar da shi gaban kotu ranar Alhamis bisa tuhumar karbar Dala biliyan $40m daga ofishin NSA
Shawarar gwamnatin tarayya na sakin sunayen wadanda suka saci kudin, martani ne ga kalubalantar da jam'iyyar PDP tayi ga gwamnatin APC na cewar ta bayyana sunayen duk wanda ya saci kudin gwamnati lokacin mulkinsu idan har suna da shaidar hakan ta faru.
Lai Muhammad yace, wannan somin-tabi ne cikin jerin sunayen barayin da suka wawuri dukiyar kasar nan.
"Ba za mu bar fadin PDP ce ta talauta kasar nan da sata ba. Sun tagayyara Nigeria. Ta kai mu yanzu bashi muke neman ciyowa daga waje. Ba kunya ba tsoron Allah suna fadin wai mu daina cewa su suka sace dukiyar kasar nan. Sai mun fada." Inji shi
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng