Ajali yayi kira: Ruwan sama kamar da bakin kwarya yayi awon gaba da wasu daliban sakandari

Ajali yayi kira: Ruwan sama kamar da bakin kwarya yayi awon gaba da wasu daliban sakandari

An tsinci gawar wasu dalibai maza guda biyu a unguwar Alagbado bayan wani ruwan sama da aka sha kamar da bakin karya a jihar Legas a ranar Alhamis 29 ga watan Maris, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu yan achaba ne suka tsinci gawarwakin yayin da ruwa yake tafiya dasu a tashar mora ta Casso, inda a tare da bata lokaci ba suka garzaya dasu zuwa Asibiti, inda a can aka tabbatar da mutuwarsu.

KU KARANTA: Ana murna bako ya tafi: Yan bindiga sun kai wani hari a Kaduna, sun kashe mutum 6

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito daya daga cikin yan Achaban wanda yace sun tsinci yaran sanye cikin kayan makarantarsu, “Ban san me suka je yi a makaranta ba, bayan an sanar da yau a matsayin ranar hutu saboda zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ga shi yanzu sun mutu.”

Ajali yayi kira: Ruwan sama kamar da bakin kwarya yayi awon gaba da wasu daliban sakandari
Ruwan sama a Legas

Sai dai wani jami’in Asibitin ya bayyana bakin cikinsa da faruwar wannan lamari, inda yace a mace aaka kawo yaran. Daga bisani wasu yan uwan yaran sun isa Asibitin, inda aka hangesu suna kuka suna ihu tare da birgima a kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel