Yanzu-yanzu: Obasanjo dan bakin ciki ne – Tinubu
Babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya siffanta wasikar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da ya rubutawa Buhari a matsayin hasada da bakin ciki kawai.
Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hakan ne a taron murna tunawa da ranan haihuwarsa da ake yi yanzu haka a jihar Legas.
A cewar Tinubu, yace: “Wasu suna rubuta wasika, wasikan hassada, sai kace basuyi shugabancin ba a baya.”
Tinibu yayi wannan furuci ne a gaban shugaba Muhammadu Buhari yayinda ya kai ziyara jihar.
Shugaba Buhari ya kai ziyaran kwana 2 ne inda zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Legas ta aiwatar karkashin jagorancin gwamna Akinwumi Ambode.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kaddamar da babban tashar Motan Ikeja
Bayan kaddamar da ayyukan, shugaban kasan ya garzaya taron lakcan bikin zagayowar ranan haihuwar babbanjigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng