Fasaha: Kamfanin Techno zai bude kamfanin kera wayoyi a Najeriya

Fasaha: Kamfanin Techno zai bude kamfanin kera wayoyi a Najeriya

- Shahararren kamfanin nan na wayar salula mai suna Techno Mobile zai kafa cibiyar sa a Najeriya don bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar daukar ma'aikata da kuma musaya a fannin fasaha

- Babban Manajan Kamfanin na Techno, Mista Chidi Okonkwo, shine ya bayyana hakan a karshen makon daya gabata, a lokacin daya jagoranci tawagar ma'aikatan kamfanin zuwa wurin Ministan Sadarwa na kasa, Mista Adebayo Shittu a Abuja

Kamfanin Techno zai bude kamfanin kera wayoyi a Najeriya

Kamfanin Techno zai bude kamfanin kera wayoyi a Najeriya

Shahararren kamfanin nan na wayar salula mai suna Techno Mobile zai kafa cibiyar sa a Najeriya don bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar daukar ma'aikata da kuma musaya a fannin fasaha.

DUBA WANNAN: Ana cigaba da yiwa bakaken fata kisan gilla a kasar Amurka

Babban Manajan Kamfanin na Techno, Mista Chidi Okonkwo, shine ya bayyana hakan a karshen makon daya gabata, a lokacin daya jagoranci tawagar ma'aikatan kamfanin zuwa wurin Ministan Sadarwa na kasa, Mista Adebayo Shittu a Abuja.

Ya bayyana cewa wayar ta Techno ta karbu sosai a ko ina a cikin Najeriya, saboda goyon bayan da kamfanin yake samu daga wurin gwamnatin tarayya, duk da haka yayi kira ga gwamnati ta cigaba da bawa kamfanin goyon baya da kuma basu tsari mai kyau domin cigaban kamfanin dama kasa baki daya. Ya kuma yi alkawarin kiyaye dangantakar dake tsakanin kamfanin da kuma gwamnatin tarayya.

Mista Okonkwo ya ce duk da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, akwai bukatar kamfanin na Techno ya kawo wani abu wanda zai kawo cigaba ga al'umma sannan kuma ya kara bunkasa tattalin arzikin kasar, hakan shine zai saka dangantakar kamfanin da gwamnatin kasar nan ta kara karfi.

Lokacin da yake magana da ma'aikatan kamfanin na Techno, Mista Shittu ya nuna farin ciki game da cigaban da kamfanin yake so ya kawo wa Najeriya, inda ya kwatanta hakan a matsayin mataki wanda zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Mista Shittu ya bayyana cewar a halin da ake ciki yanzu kasar nan ta zama tamkar kasuwa wacce kasashen waje suke shigowa domin baje kolin su, inda hakan ba karamin ci baya bane ga gwamnatin kasar. Sannan ya ce gwamnati tana bukatar ta bunkasa samar da kayan gida ta kowanne fanni wanda zai cigaba ga matasan mu.

Ministan ya kara da cewar gwamnatin tarayya zata yi iya yin ta domin ganin kudurin da kamfanin ya dauka ya karbu a kasar nan, saboda hakan ba karamin cigaba bane zai kawo a fannin fasaha a kasar nan.

A karshe Mista Shittu ya yabawa kamfanin da kokarin da yake, inda ya bayyana cewar idan har kudurin ya karbu to akwai yiwuwar a samawa matasa sama 3500 aiki a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel