An kama matsafi da kayuwan mutane uku a Ilorin

An kama matsafi da kayuwan mutane uku a Ilorin

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Mista Lawan Ado, ya ce sun kama mutumin mai suna Suleiman Adenifuja da kokon kai guda uku ranar 26 ga watan Maris, a yankin Ogbomosho-Eiyekorin a garin Ilorin.

Ado ya ce, mutumin ya bayyana masu cewar ya samo kokon kan mutanen ne a jihar Legas domin yin wasu aiyukan tsatsuba da su.

Kazalika kwamishinan ya ce, jami'an hukumar sun yi nasarar cafke mutum, Wahab Ramoni, da wata motar sata kirar Toyota Camry, mai lamba; AKD 287 EE tare da bayyana cewar zasu mika motar ga mai ita da zarar sun kammala bincike.

An kama matsafi da kayuwan mutane uku a Ilorin
Shugaban hukumar 'yan sanda; Ibrahim K. Idris

A wani labarin Legit.ng, kun karanta cewar, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta kama wani mutum dake aikin leken asiri ga kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram a garin Wudil, ranar 24 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: An kama dan leken asirin kungiyar Boko Haram a Kano

Mutumin, Sanusi Bello, an kama shi da wayoyin hannu da kuma katinan shaidar aiki masu yawa, ciki har da na hukumar 'yan sandan Najeriya da kuma na wani makwabcinsa dan kungiyar bijilanti da kudi, N37,857.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: