Nigerian news All categories All tags
Wani Ango ya fada komar Yansanda bayan ya saci mota don ya samu kudin bikin aurensa

Wani Ango ya fada komar Yansanda bayan ya saci mota don ya samu kudin bikin aurensa

Wani tsohon direba mai suna Mohammed Chado ya fada komar Yansanda bayan an kama shi da laifin satar wata mota da aka bashi ya wanke, wanda ya siyar da nufin biyan sadakin aurensa da daukan nauyin biki.

Daily Trust ta ruwaito barawon ya bayyana ma yan jarida cewar wannan ne karon farko da ya taba satar mota, inda ya kara da cewa ya kasance tsohon direba ne a baya, kafin ya fara aikin wankin mota.

KU KARANTA: Yadda wani karamin Yaro ya tsallake rijiya da baya a hannun masu yankan kai a birnin Kebbi

“Ko shago bani da shi, ina maleji ne a kauyen Apo, amma da suka bani motar kirar Toyota na wanke ne, sai na yi awon gaba da ita, inda na siyar, kuma na yi amfani da kudin wajen yin aure” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Sadiq Bello yana fadin a ranar 7 ga watan Maris ne jami’an Yansanda suka cafke Chado a kauyen Bafete na jihar Neja, indaya boye bayan ya cefanar da motar akan kudi naira dubu dari hudu da hamsin (N450,000).

Sai dai Kwamishinan yace sun samu nasarar kwato motar, sa’annan ya kara da cewa rundunar Yansandan ta samu nasarar kama wasu gagararrun yan fashi da suka kware wajen afkawa gidajen mutane, bayan sun yi sata a cocin RCCG dake Mabushi, inda suka kwashe talabijin 5, na’urar dauka hoto da fankoki.

Bello ya bayyana sunayen barayin kamar haka: Munir Abdullahi mai shekaru 26, Hayatu Ya’u mai shekaru 29, Muhammed Isah mai shekaru 33, Abba Bashir mai shekaru 27 da Salisu Muhammed mai shekaru 29.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel