Burin wasu ma'aurata ya cika sun mutu a rana daya

Burin wasu ma'aurata ya cika sun mutu a rana daya

- Burin wasu ma'aurata da suka shafe sama da shekaru 63 da yin aure ya cika inda suka mutu a rana daya. Edna Huntley mai shekaru 81 ta mutu ranar 20 ga watan Maris dinnan jim kadan bayan ta kwanta bacci, yayinda shima mijinta Bob Huntley mai shekaru 83 ya ce ga garinku nan awa daya bayan matar tashi ta mutu

Burinsu wasu ma'aurata ya cika sun mutu a rana daya
Burinsu wasu ma'aurata ya cika sun mutu a rana daya

Burin wasu ma'aurata da suka shafe sama da shekaru 63 da yin aure ya cika inda suka mutu a rana daya. Edna Huntley mai shekaru 81 ta mutu ranar 20 ga watan Maris dinnan jim kadan bayan ta kwanta bacci, yayinda shima mijinta Bob Huntley mai shekaru 83 ya ce ga garinku nan awa daya bayan mutuwar matar tashi.

DUBA WANNAN: Kunji wani shi kuma: Yana garkuwa da mutane domin ya kara jarin shagon sa

A kwanakin baya ne aka bayyana wa Edna cewar tana dauke da Cutar Daji, inda shi kuma Bob aka bayyana mashi cewar yana da cutar gigin tsufa, a rahoton jaridar "Press Tribune" Edna ta taba gayawa wata kawarta cewar; "Duk ranar da daya daga cikin mu ya mutu to na tabbata baza a kaishi kabari shi kadai, face sai dayan ya biyo shi. Kuma abinda ya faru kenan."

Wani daga cikin 'yayansu da suka mutu suka bari Kenneth Huntley, ya bayyana wa manema labarai cewar; "Mun ji dadi sosai da wannan lamari ya faru, saboda gaskia da bamu san halin da mahaifinmu zai shiga ba idan har baya tare da Edna."

Bob da Edna Allah ya albarkace su da samun 'ya'ya biyar, maza biyu mata uku, sai jikoki guda 43.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng