Kuma dai: Cikin awanni 24 Yan bindiga sun kai hari wani kauye sau biyu, sun kashe 25
Gungun wasu Yan bindiga, da ake zaton yaran tsohon kasurgumin dan bindigan nan ne, Buharin Daji, wanda aka kashe a kwanakin baya, sun kai farmaki wani kauyen jihar Zamfara sau biyu cikin awanni 24.
Maharani sun kai hare haren ne a kauyen Bawardaji dake cikin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane sama da ashirin da biyar, tare da raunata da dama, inji rahoton BBC Hausa.
KU KARANTA: Gwamnan jihar Taraba ya nuna ma Buhari yatsa game da matsalar tsaro data dabaibaye jihar
Wani mazaunin kauyen, ya shaida ma majiyar Legit.ng cewar a yayin harin farko da suka kai kauyen a ranar Talata 27 ga watan Maris, yan bindigan sun kashe mutane 13.
Bayan wasu awanni kadan suka sake komawa kauyen na Bawardaji, da safiyar ranar Laraba 28 ga watan Maris, inda suka kashe mutane 12 a wani harbin mai kan uwa da wabi da suka yi, a daidai lokacin da ake gudanar da jana’izar mamatan da suka kashe a harin farko.
Jihar Zamfara dai ta dade tana fama da matsalolin tsaro da suka danganci hare haren barayin shanu, wanda hakan ya durkusar da tattalin arzikin jihar daya dogara kacokan ga aikin noma. Ko a baya sai da wani dan majalisa ya zargi gwamnan jihar Abdul Aziz Yari da sanin maharan, sai dai ya musanta zargin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng