Kunji wani shi kuma: Yana garkuwa da mutane domin ya kara jarin shagon sa
- Garkuwa da mutane domin kudin fansa ya zama tamkar ruwan dare a kasar nan, musamman ma a kudancin kasar nan, to sai dai yanzu yankin arewa abin ba a cewa komai, domin suna nan sunyi wa yankin kaka gida. A wannan satin ne rundunar 'yan sandan jihar Niger tayi nasarar kama kimanin mutum 11 da laifin fashi, garkuwa da mutane da kuma satar shanu, ciki kuwa hadda wani wanda yace shi yana sana'ar satar mutanen ne domin ya kara jari a shagon sa.
A ranar Talatar nan ne rundunar 'yan sanda ta jihar Niger, ta kama wasu mutane su 11 da zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma satar shanu.
DUBA WANNAN: Dalilan da suka sa Usman DanFodio fara Jihadi a Arewacin Najeriya
A lokacin daya ke zantawa da manema labarai, mai magana da yawun rundunar, ASP Muhammad Abubakar, ya ce a kokarin da hukumar take na ganin ta dakile amfani da makamai, da kuma sayar dasu, wanda shine musabbabin abinda yake kawo kashe-kashe, fashi da makami, satar mutane da kuma satar shanu a yankin jihar, rundunar 'yan sandan ta kama wani mutumi mai suna Ayuba John wanda ya kware wurin kera makamai. Rundunar ta samu nasarar binciko wasu mutane biyar wadanda suke da alaka dashi, sune kamar haka:
1. Abdullahi Naliman mai shekaru 45
2. Abubakar Shehu mai shekaru 43
3. Ali Usman mai shekaru 23
4. Mohammed Rufa'i mai shekaru 28
5. Umar Mohammed Babuga mai shekaru 35
Dukkan su daga kauyen Saminaka dake karamar hukumar Lapai, wadanda kuma sune ake zargin suka yiwa Alhaji Bako fashi na babur nashi kirar Bajaj, a karamar hukumar Lapai, inda daga baya suka kirashi suka bukaci ya basu dubu 400 ko kuma su zo su sace shi, inda shi kuma cikin gaggawa ya je ya basu kudin.
An samu wadanda ake zargin da makamai wadanda suka hada da; Bindigogi, Harsashi, da dai sauran makamai masu hadari.
Rundunar 'yan sandan ta samu nasarar kama wani mai suna Lucky Simon mai shekaru 34 a kauyen Jamaku dake karamar hukumar Mashegu, wanda ya addabi jama'ar yankin da satar mutane domin neman kudin fansa, wanda ake zargin ya bayyana cewar yana satar mutanen ne saboda yana son ya samu kudin da zai kara jarin shagon maganin shi.
A karamar hukumar Rijau kuma rundunar ta kara samun nasarar kama wasu mutane biyu Saminu Adamu daga jihar Zamfara da kuma Umaru Ali daga kauyen Gashiwa dake jihar Nasarawa, inda aka kama su da shanu 16 da suka sace. Sannan ta kara kama wani mai suna Bawa Hakumi mai shekaru 28, shima an kama shi da laifin satar shanu.
Duka masu laifin sun amsa laifin su, inda suka tabbatar wa da hukumar 'yan sanda cewar sun aikata laifin da ake tuhumar su dashi, sannan hukumar 'yan sandan ta bayyana cewar zata gurfanar dasu a gaban kotu da zarar ta gama bincike akan su.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng