Biki yayi biki: An kama Sanatocin Najeriya yayin da suke tikar rawa a bikin diyar Dangote (Bidiyo)
Mazari sarkin rawa, kamar yadda Hausawa ke kiran duk wani dan ‘ina da rawa.’ Kwatankwacin haka ne ya faru a yayin bikin hamshakin attajiri, Aliko Dangote, inda wasu manyan mutane suka barje gumi, kamar yadda Legit.ng ta gano.
Manyan mutanen kuwa sun hada da wani wakilin al’ummar Kogi ta yamma a majalsar dattawa, Sanata Dino Melaye, da kuma wakilin jama’an jihar Osun duk a majalisar na dattawa, Sanata Adeleke.
KU KARANTA: Yadda ta kwashe a tsakanin Ganduje da wani karamin yaro mai nakasa da mahaifinsa ya bar masa wasiyya ga Gandujen
Ga bidiyon rawar
Dama dai Sanata Adeleke yayi kaurin suna wajen tikar rawa son ransa, a duk inda ya ji kida, kodayke dai babu mamaki, tunda bincike ya tabbatar da cewar shi ne kawun shahararren mawakin Najeriya, Davido.
A yayin bikin an hangi Sanata Melaye da Sanata Adeleke suna goge raini a wani yanayi na ‘wa ya fini iya rawa.’ Ko kuma ace ‘Idan ka iya ka taka’, inda jama’a suka zagaye su suna kallonsu, ana shewa, ana tafi.
Ga wani bidiyon ma:
A wani labarin kuma, Dino Melaye ya arce daga Najeriya sakamakon nemansa da wata babbar Kotun babban birnin tarayya ta yi don ya gurfana a gabanta, biyo bayan tuhume tuhumen da ake masa na baiwa wasu bata gari muggan makamai da nufin tayar da zauni tsaye.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng