Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya data daina kama masu shan tabar wiwi

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya data daina kama masu shan tabar wiwi

- A ranar Litinin dinnan ne Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Gwamnatin Najeriya data sassauta hukunci akan masu amfani da tabar wiwi a nan gaba

- Virk ta ce tabar wiwi magani ce sadidan da ake amfani da ita domin warkar da marasa lafiya amma ba wai domin asha a bugu ba

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya data daina kama masu shan tabar wiwi
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya data daina kama masu shan tabar wiwi

A ranar Litinin dinnan ne Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Gwamnatin Najeriya data sassauta hukunci akan masu amfani da tabar wiwi a nan gaba.

DUBA WANNAN: Dalibar da aka zuba wa Acid ta samu sauki

Majalisar kuma ta bukaci a daina daukan masu amfani da amfani da tabar a matsayin masu laifi, musamman ma wadanda suke amfani da ita domin magani, kaman yanda mafi yawa daga kasashen duniya suke daukan shan tabar wiwin a mtsayin laifi mai girma.

Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta bangaren miyagun kwayoyi da manyan laifuka, Harsheth Kaur Virk, ta bayyana matsayin da duniya ta sanya tabar wiwi din game da amfanin ta a jikin Dan Adam, ta yi bayanin ne a lokacin data halarci wani taro akan hadarin amfani da miyagun kwayoyi ga matasa a Najeriya, wanda kwamitin Majalisar Dattijai ta shirya.

Virk ta ce tabar wiwi magani ce sadidan da ake amfani da ita domin warkar da marasa lafiya amma ba wai domin asha a bugu ba.

Ta ce: "Ofishin yaki da kwayoyi da manyan laifuka na Majalisar Dinkin Duniya suna ganin masu amfani da miyagun kwayoyin babbar barazana ce ga rayuwar su, inda shan kwayar yake jawo musu ciwuka kala - kala."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng