Kaje ka kare kanka a gaban hukuma, ba ruwana da harkar ka - Yahaya Bello ya gargadi Dino Melaye
- A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kingsley Fanwo, ya fitar, gwamnan ya shawarci Sanatan da yayi kokari ya bayyana gaban hukumar 'yan sanda domin ya kare kanshi akan zargin da ake yi masa
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya maidawa Sanata Dino Melaye martani, wanda yake zargin cewa gwamnan yana amfani da hukumar 'yan sanda ne domin suga bayan shi. Yayinda shi kuma gwamnan ya bukaci Sanatan da ya kyale shi yaje yaji da matsalar shi da 'yan sanda.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta fara zama na neman sulhu da 'yan Boko Haram
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kingsley Fanwo, ya fitar, gwamnan ya shawarci Sanatan da yayi kokari ya bayyana gaban hukumar 'yan sanda domin ya kare kanshi akan zargin da ake yi masa.
Mai magana da yawun gwamnan, ya kara da cewar abu mafi sauki da ya kamata Sanatan yayi shine yaje ya kare kanshi, sannan ya daina saka gwamnan a cikin damuwar shi.
"Yaje ya fuskanci hukuma ya fitar da gwamna a cikin damuwarshi. Saboda gwamna mutum ne mai bin dokar kasa wanda ba zai taba saka kansa a cikin irin wannan ta'asar ba. Sannan kuma babu wata kungiya data taba zargin gwamnan mu da irin wannan laifin naka."
"Ya san darajar al'umma. Saboda haka babu ruwan gwamna a cikin aikin ta'asar ka. Hukumar 'yan sanda sun kama 'yan ta'adda, su kuma 'yan ta'adda da suka ji wuya sai suka tona asirin wanda ya saka su. Mun tabbata cewar Yahaya Bello mutum ne wanda yake kishin rayukan al'ummar jihar Kogi. Kuma shine ya bawa hukumar 'yan sanda umarnin su kama duk wani wanda yake da hannu akan ta'addancin da ake yi a jihar nan. Saboda haka Dino yaje ya fuskanci hukuma domin kare kanshi."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng