‘Yan Majalisa sun binciko wata badakala da aka tafka a 2013 da 2014
- Majalisa tace an karkatar da wasu kudi a Hukumar NIPC a kwanakin baya
- Wani kwamitin Majalisar Wakilai tace dole a maidawa Gwamnati kudin ta
- Shugabar Hukumar tace ba ta nan lokacin da aka tafka wannan badakalar
Mun samu labari cewa Majalisar Tarayya ta nemi Hukumar NIPC da ke lura da masu zuba hannun jari a Najeriya ta maido wasu makudan kudi da su ka kusa kai rabin Biliyan zuwa asusun Gwamnati.
Wani kwamiti na Majalisar Wakilan Tarayya yayi bincike inda ya gano cewa Hukumar NIPC tayi awon-gaba da Naira Miliyan 477 da ta tara a shekarar 2013 da 2014 a lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yana mulki.
KU KARANTA: An gano 'Yan ta'addan da ke kashe jama'a a Najeriya
‘Yan Majalisar sun ce dole a maidawa Gwamnatin Najeriya wannan makudan kudi bayan da Akanta-Janar na kasar ya fara kai kuka tun kwanakin baya. Sakatariyar Hukumar Yewande Sadiku tace ba ta san lokacin da abin ya faru ba.
Majalisar Kasar ta kuma nemi Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa su binciki lamarin cikin watanni 2 a kuma maidawa asusun Gwamnatin Najeriya kudin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng