Mutuwar Sanata Ali Wakili: Osinbajo ya ziyarci jihar Bauchi domin mika sakon ta'aziyya

Mutuwar Sanata Ali Wakili: Osinbajo ya ziyarci jihar Bauchi domin mika sakon ta'aziyya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai ziyara jihar Bauchi, domin mika ta'aziyya ga gwamnatin jihar, masarautar jihar, mutanen jihar da kuma iyalan marigayi Sanata Ali Wakili.

Mista Osinbajo, wanda ya samu tarya daga duban masoya maza da mata masu masa fatan alkairi, ya ziyarci Mai martaba Sarkin Bauchi Alh. Dr. Rilwanu Suleiman Adamu fadar sa, inda ya ce ya zo fadar ne domin isar da sakon ta'aziyyar sa na babban rashin da aka yi na Sanata Ali Wakili, inda mataimakin shugaban kasan ya ce wannan rashin ba na jihar Bauchi bane kadai,rashi ne ga kasa baki daya.

Osinbajo ya ce za a tuna da Sanata Wakili, musamman ma yadda ya yi aiki tukuru dama bayar da gudumawan sa a shugaban kwamitin yaki da talauci na majalisar kasa.

Daga karshe Osinbajo ya ziyarci gidan marigayin inda ya isar da sakon ta'aziyyar sa ga iyalansa.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta daure wanda ke sojan gona da sunan sarkin kano na tsawon watanni 36

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata babban tawaga da daga majalissar dattawan Najeriya karkashin jagorancin, Sanata Bukola, sun kai ziyarar ta’aziya ma Gwamnatin Bauchi Sarkin Bauchi da iyalin marigayi Ali Wakili akan mutuwar abokin su.

Allah yayi wa Sanata Ali Wakili rasuwa ne a ranar Asabar da gabata a birnin Abuja bayan ya yanke jiki ya fadi bayan kirjin sa ya buga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng