Birai sun addabi mazauna wani kauye ya kai ga sun gudu sun bar musu garin

Birai sun addabi mazauna wani kauye ya kai ga sun gudu sun bar musu garin

- Al'ummar wani kauye dake jihar Legas sun shiga wani hali sanadiyyar wasu Birai da suke shigo musu garin a duk lokacin da suka ga dama suyi musu barna su gudu

- Jama'ar garin sun koka akan halin da suke ciki inda suke rokan gwamnatin jihar Legas data kawo musu dauki

- Mazauna garin sun bayyana cewar zaman garin yayi musu wahala inda tilas tasa ka suka bar garin saboda basu da damar ajiye abinci ko wani abu mai amfani sai sun zo sun lalata shi

Birai sun addabi mazauna wani kauye ya kai ga sun gudu sun bar musu garin
Birai sun addabi mazauna wani kauye ya kai ga sun gudu sun bar musu garin

Shigowar Birai cikin wani yanki na jihar Legas ya tilasta wa mazauna garin Soluyi/Sosanya Gbagada, guduwa daga garin. A ranar Litinin din nan ne wasu daga cikin mazauna garin suka shaidawa manema labarai a jihar Legas cewa baza su iya cigaba da zama a garin ba.

DUBA WANNAN:

Mazauna garin sunyi kira ga gwamnatin jihar data kawo musu dauki domin ceto su daga matsalar da suke ciki, inda suke bayyana cewa dabbobin suna karya kofofin su ta karfi suna shiga dakunan su lalata musu kayan abinci da sauran abubuwan amfani na rayuwa.

Shugaban mazauna kauyen Mista Adigun Olaleye ya ce a yanzu haka zaman garin ya zame wa da yawa daga cikin al'ummar garin matsala, saboda barnar da suke yi musu.

Ya ce shigowar dabbobin kauyen nasu yana da alaka da irin kusancin da suke dashi da wani daji wanda yake dauke da muggan dabbobi. Sannan ya kara da cewar, Biran sukan shigo kauyen ne a kowanne lokaci da suke so sannan kuma sukan karya kofofin su shiga dakunan su suyi musu barna.

Mista Olalaye ya shaidawa manema labarai cewa mazauna garin sun rubuta wa Ma'aikatar Aikin Gona ta jihar Legas wasika akan irin halin da suke ciki, amma har yanzu ba wanda ya kawo musu wani dauki.

"Sun ce sai mun biya su sannan zasu zo su kwashe biran da suka addabe mun," inji shi. Ya kara da cewar yanzu kusan shekara daya kenan suna fuskantar wannan matsalar, inda a yanzu haka abin ya fi karfin su.

A karshe Mista Olaleye ya roki gwamnatin jihar Legas data kawo musu dauki akan matsalar da suke ciki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng