Labari mai ban tausayi: Yadda ta kwashe a tsakanin Ganduje da wani karamin yaro mai nakasa da mahaifinsa ya bar masa wasiyya ga Gandujen

Labari mai ban tausayi: Yadda ta kwashe a tsakanin Ganduje da wani karamin yaro mai nakasa da mahaifinsa ya bar masa wasiyya ga Gandujen

Wani abin tausayi ya faru a tsakanin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da wani karamin yaro mai nakasan kafa a ranar asabar 24 ga watan Maris, wanda ya baiwa jama’an dake wajen mamaki matuka.

Wannan lamari dai ban cike da darasa ya faru ne a garin Rano dake jihar Kano, yayin da Ganduje ya kai ma tsohon kakakin majalisa kuma Turakin Rano Alhaji Kabiru Rurum a gidans, kwatsam sai ga wani yaro mai larurar ya tunkaro kujerar manyan baki, watau inda gwamna ke zaune.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Rukayya Dawayya ta yi karin haske game da matsalar da ta yi sanadin mutuwar aurenta

Ma’abocin kafar sadarwar zamani Uba Danzainab ne ya bayyana lamarin kamar yadda ya faru a gabansa, inda tausayin yaron ya kama jami’an tsaron gwamna Ganduje, suka kyale shi ya karasa, sa’annan suka tambayeshi abinda ke tafe da shi, sa’annnan suka bashi damar isa ga gwamna.

Labari mai ban tausayi: Yadda ta kwashe a tsakanin Ganduje da wani karamin yaro mai nakasa da mahaifinsa ya bar masa nasiyya ga Gandujen
Yaron da Ganduje

Majiyar Legit.ng ya cigaba da fadin da isarsa wajen gwamna, sai Yaron ya bayyana masa cewa mahaifinsa na daga cikin wadanda suka amfana da tallafin shayi da Gwamna ya baya a yan kwanakin baya.

Sai dai kash Allah yayi masa rasuwa, “don haka ne ma kafin mutuwarsa ya umarceni ta hanyar barin mini sakon wasiyya, da cewa duk indsa naga gwamna, in sanar da shi cewar har ya mutu yana godiya da tallafin shayin da ya bashi, wanda ya tallafa ma rayuwarsa da ta iyalinsa.”

Labari mai ban tausayi: Yadda ta kwashe a tsakanin Ganduje da wani karamin yaro mai nakasa da mahaifinsa ya bar masa nasiyya ga Gandujen
Yaron da kudin da Ganduje ya bashi

Shi kuwa gwamna Ganduje bayan kammala sauraron wannan yaron, sai ya sanya hannunsa cikin aljihu, inda ya zaro bandir din kudi N50,000 ya baiwa wannan yaro, tare da umartarsa da yaje ya cigaba da wannan sana’a, kuma ya kula da kannensa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng