Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya (hotuna)

Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya (hotuna)

- A kokarin da yankin Afirika ta Yamma suke na ganin sun kawo zaman lafiya a kasashen dake yankin, a yaune Sojojin Najeriya suka nufi kasar Gambia domin taimakawa wurin kwantar da tarzoma

- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya tayi aikin jigilar Sojojin zuwa kasar ta Gambia, tare da kayan aikinsu, hukumar ta daukesu ne daga filin jiragen sama na birnin tarayya

A kokarin da yankin Afirika ta Yamma suke na ganin sun kawo zaman lafiya a kasashen dake yankin, a yaune Sojojin Najeriya suka nufi kasar Gambia domin taimakawa wurin kwantar da tarzoma.

Hukumar Sojojin Saman ta Najeriya (NAF) tayi aikin jigilar Sojojin Kasa, dana Ruwa zuwa kasar ta Gambia tare da kayan aikinsu domin su bayar da agaji wurin kwantar da tarzomaa kasar.

Hukumar ta daukesu ne daga filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe, dake birnin tarayya zuwa filin jiragen sama na Banjul a kasar Gambia.

Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya (hotuna)
Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya

Kuma ana sa ran cewa Sojojin saman zasu dawo da Sojojin da sukayi watanni shida a kasar ta Gambia suna aikin bayar da agaji domin a canjesu da wasu sajojin.

Sojojin saman sun kasance na farko da suka fara kai agaji a kasar ta Gambiya, a watan Janairu, shekara ta 2017, a matsayin agajin farko da kungiyar ta kasashen Afirika ta Yamma suke bayarwa don kula da ayyukan zabe na ranar 1 ga watan Disamba, shekara ta 2016, wanda shuwagabannin kungiyar na jihohi suke tallafawa dashi. Wanda hakan ya sake mayar da Adama Barrow, a matsayin shugaban kasa.

Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya (hotuna)
Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya

Hukumar ta Sojojin saman ta bayar da mutane 200, da kayan aiki, wanda suka hada da Jiragen Yaki, Jirgin daukar mutane da kaya, Jirage masu saukar Angulu, tare da na’urorin bincike.

KU KARANTA KUMA: A kullun ina rayuwa cikin dar-dar – Melaye

Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya (hotuna)
Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya

Bada agajin na Sojojin Sama ya tallafawa kasar sosai wurin ganin cewa an karbi mulki daga hannun tsoho shugaban kasar, Yahya Jammeh, wanda yayi murabus a ranar 21 ga watan Janairu, shekara ta 2017, wanda hakan ya dawo da martabar siyasa a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng