Mutane 5 sun hallaka, da dama sun jikkata yayinda Boko Haram suka bude wuta a cikin Kasuwa

Mutane 5 sun hallaka, da dama sun jikkata yayinda Boko Haram suka bude wuta a cikin Kasuwa

Akalla mutane 5 sun rasa rayukansu kuma da dama sun jikkata yayinda yan ta’addan Boko Haram suka kai hari kudu maso gabashin kasar Nijar jiya Juma’a , 23 ga watan Maris, 2018.

Wani mazaunin Toummour, a yankin Diffa ya bayyana cewa: “Yan Boko Haram sun shigo kasuwa da yammacin Juma’a inda suka harbi mutane suka kwashe kayan abinci,”

Wani jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa mutane 5 ne suka rasa rayukansu.

Gwamnan Diffa, Mahamadou Laoualym ya garzaya garin Toummour ranan asabar domin gaisuwan ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu kuma ya yi kira ga hukumar soji da ke bibiyan yan ta’addan.

Mutane 5 sun hallaka, da dama sun jikkata yayinda Boko Haram suka bude wuta a cikin Kasuwa
Mutane 5 sun hallaka, da dama sun jikkata yayinda Boko Haram suka bude wuta a cikin Kasuwa

“Muna ba mutane hakuri .. Wannan shekara ne na yaki da Boko Haram”

A watan Junairu, an hallaka jami’an sojin kasar Nijar 7 kuma an jikkata 17 a wani hari a Toummour da ke yammacin Diffa kusa da tekun Chadi.

Diffa tana fuskantan hare-haren Boko Haram tun lokacin da abun ya tsallaka kasar a 2015.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: