Ku mayar da hankali ga addu’a – Kungiya ga gwamnatin tarayya

Ku mayar da hankali ga addu’a – Kungiya ga gwamnatin tarayya

- Kungiyar ta bukaci ‘yan Najeriya dasu tallafawa Najeriya da addu’a don samun mafita bisa ga matsalolin da kasar ke fuskanta

- Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Mohammaed, ya bayar da wannan shawara lokacin da suka gabatar da taro na musamman don yiwa kasa addu’a

- Mohammed yace, babu wata matsala da baza’a iya maganceta ta hanyar addu’a ba

Kungiya Jma’atul Ibadat Wazikirullahi ta bukaci ‘yan Najeriya dama gwamnati dasu tallafawa kasar da addu’a don samun mafita ta har abada, bisa ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Mohammaed, ya bayar da wannan shawara ne a ranar Lahadi, a Maraba dake karamar hukumar Karu, a jihar Nasarawa, lokacin da suka gabatar da taro na musamman don yiwa kasa addu’a.

Mohammed yace, babu wata matsala dake damun dan Adam wadda baza’a iya maganceta ta hanyar addu’a ba.

Ya kara da cewa, tun farkon tashe-tashen hankula a wasu yankunan kasar, gwamnati bata mayar da hankali wurin yiwa kasar addu’a ba, sai dai ta kashe kudade dayawa ta fannin samar da makamai ga jami’an tsaro.

Ya bayyana cewa, kungiyar a shirye take don ganin ta wa’azantar da mutane talakawa, marayu, almajirai, da wadanda ke daure a gidan yari, akan muhimmancin zaman lafiya a kasa.

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojojin Najeriya sun tafi Gambia domin marawa kudirin ECOWAS baya (hotuna)

Shugaban kungoyar Dariqatul Tijjaniya na birnin tarayya, Sheikh Abubakar Shu’aibu, ya bukaci musulmai dasuyi koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), wanda ya koyar damu son juna, da hakuri da juna, da kuma kula da hakkin makwabtaka.

Yace, “Ina bawa musulmai shawara da suyi koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), na zaman lafiya da wadanda ba musulmi ba”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng