An yi wa wani tsohon Sanatan Arewa Mubaya’a ya gwabza da Buhari a 2019

An yi wa wani tsohon Sanatan Arewa Mubaya’a ya gwabza da Buhari a 2019

- Wasu Matasa su na nema Sanata Baba Ahmed ya fito takarar Shugaban kasa

- Matasan sun ce babu wanda ya dace da mulkin Najeriya kaf irin Yusuf Datti

- Da alamu tsohon Sanatan na Jihar Kaduna na shirin tsayawa takara a 2019

Mun samu labari cewa wasu Matasan Kasar nan karkashin lemar CNY sun tsaida tsohon Sanatan Kaduna ta Arewa Yusuf Datti Baba Ahmed a matsayin ‘Dan takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019.

An yi wa wani tsohon Sanatan Arewa Mubaya’a ya gwabza da Buhari a 2019
Ana tunzura Sanata Baba Ahmad ya fito takara a 2019

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wasu Matasa masu kishin kasar nan sun yi wani taro a Birnin Tarayya Abuja inda su kayi na’am da cewa Sanata Baba Ahmed ya cancanci ya tsaya neman kujerar Shugaban kasa a zaben 2019.

KU KARANTA: Atiku yayi wa Matasa alkawari idan ya ci Shugaban kasa

Matasan sun bayyana cewa Baba Ahmed ‘Dan siyasa ne mai jama’a kuma wanda ake ganin kimar sa. Sani Danbarno wanda shi ne Shugaban wannan kungiyar ta Matasa yace sun yanke shawarar Baba Ahmed ya fito takara.

Sani Danbarno yace da su ka duba sauran masu neman kujerar Shugaban kasar a 2019 sun gano cewa babu wanda ya cancanta irin Sanata Yusuf Datti Baba Ahmed saboda irin kokarin sa da kuruciya da kuma sanin aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng