Sojojin Saudiyya sun samu nasarar dakatar harin makamai masu linzami guda 7 na 'yan tawayen Houthi

Sojojin Saudiyya sun samu nasarar dakatar harin makamai masu linzami guda 7 na 'yan tawayen Houthi

- A wani bidiyo da aka aikawa kafar yada labarai ta Al-Arabiya ya nuna abinda ya faru a lokacin da aka harba makamai masu linzamin daga kasar ta Saudiyya domin aika sako ga 'yan ta'addar Houthi akan su cire makaman su akan birnin na Riyadh

Sojojin Saudiyya sun samu nasarar dakatar harin makamai masu linzami guda 7 na 'yan tawayen kabilar Houthi
Sojojin Saudiyya sun samu nasarar dakatar harin makamai masu linzami guda 7 na 'yan tawayen kabilar Houthi

A ranar Lahadi din nan ne jami'an rundunar sojin kasar Saudiyya suka samu nasarar dakatar da harin makamai masu linzami guda 7 da 'yan tawayen Kabilar Houthi suke shirin harbawa, ciki harda daya a birnin Riyadh.

DUBA WANNAN: Fitowa takarar Buhari na biyu ba a hannun Dattawan Arewa yake ba

"Wani mai magana da yawun rundunar sojin kasar Turki Al-Malki ya ce, tashin hankalin da ake samu a yankin nasu ya biyo bayan goyon bayan da kasar Iran take bawa 'yan tawayen Kabilar ta Houthi".

Shaidu sun bayyana wa kafar yada labarai ta Al-Arabiya cewa an samu fashewar wani abu mai kara da kuma haske sosai a sararin samaniya.

A wani bidiyo da aka aikawa kafar yada labarai ta Al-Arabiya ya nuna abinda ya faru a lokacin da aka harba makamai masu linzamin daga kasar ta Saudiyya domin aika sako ga 'yan ta'addar Houthi akan su cire makaman su akan birnin na Riyadh.

Tun watan Nuwamba, Yemen da Iran suka hada kai da 'yan tawayen Houthi suka dinga harba makamai masu linzami zuwa kasar ta Saudiyya, duk da cewar sojojin Saudiyyar suna yin iya bakin kokarin su wurin dakatar da hare-haren nasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng