Shugaban kungiyar Kiristocin jihar Taraba ya kwanta dama a wata mummunan yanayi
- Shugaban kungiyar Kiristocin jihar Taraba ya kwanta dama a wata mummunan yanayi
- Mamacin ya taba yi hasashen mutuwar Buhari a lokacin da bashi da lafiya
Allah Sarki, Duniya kenan, a yayin da kake naka, Allah ya riga yayi nasa, kwatankwacin lamarin da ya faru kenan a jihar Taraba, inda wani Fasto da yayi hasashen mutuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2014 ya riga Buharin cikawa.
Wannan Fasto mai suna Ben Ubeh, shi ne shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, reshen jihar Taraba, kuma ya mutu ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Maris a sakamakon wani mummunan hadari d aya rutsa da shi.
KU KARANTA: Sakin yan matan Dapchi: Iyayen yan matan Chibok sun garzaya wajen Obasanjo
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan hadari da yayi ajalin Ubeh ya faru ne tsakaninsa da wata babbar motar daukan kaya a kan babban hanyar Jalingo zuwa Yola, a garin Zing, inda motar ta mutsutstsuke namarsa a kan titi.
Sai dai sakamakon munin hadarin, daga bisani jama’an dake wajen suka zuba kasa, daga nan kuma suka tattara abinda ya ragu a cikin buhu, inda aka garzaya da shi zuwa garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng