Fitowa takarar Buhari na biyu ba a hannun Dattawan Arewa yake ba
- Wani dan takarar gwamnan jihar Abia a karkashin jam'iyyar APC, Prince Okey Chemberline Adiaso, ya bayyana cewar, fitowa takarar shugaba Muhammadu Buhari na biyu baya dogara ne akan iya shugabannin Arewa ba ne kawai
Wani dan takarar gwamnan jihar Abia a karkashin jam'iyyar APC, Prince Okey Chemberline Adiaso, ya bayyana cewar, fitowa takarar shugaba Muhammadu Buhari na biyu baya dogara ne akan iya shugabannin Arewa ba ne kawai.
DUBA WANNAN: Sama da mutane 20 suna zawarcin kujerar Ali Wakili
A cikin jawabin da yayi ya bayyana wasu kungiyoyi a Arewa, ciki har da kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) da kuma Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) cewar suna neman wani dan takarar saboda suna ganin cewar shugaba Buhari ya kasa rike Najeriya, Mista Adiason ya ce a yanzu haka duk Najeriya babu kamar shugaba Muhammadu Buhari.
Yayin da yake bayani ga manema labarai a kauyen sa Obichukwu a karamar hukumar Ngwa na jihar Abia bayan ya bayyana manufar sa ta yin takarar gwamna a zabe mai zuwa na 2019, ya ce abin da shugabannin arewa suke fada ra'ayinsu ne kawai wanda hakan ba yana nufin ra'ayin duka 'yan arewa bane.
Ya bayyana ra'ayin nasu akan soki burutsu ne, saboda ko shugabannin adawa sun san da cewar shugaba Buhari yayi abin a zo a gani a kasar nan.
Mista Adiason, ya nuna cewar yayi bayanin ne bisa hangen nesa da kuma cancanta irin ta shugaba Muhammadu Buhari, inda ya kara da cewar irin wannan hangen nesan ne ya sa shi fitowa takarar gwamnan a jihar ta sa domin ya fito da jihar dag cikin kangin da ta shiga na rashin cigaba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng