An yi mana irin abin da aka yi wa ‘Yan Kwankwasiyya a Kano – PDP
- PDP ta koka da Gwamnatin Jihar Kano bayan an hana ta wani gangami
- Jam’iyyar adawar tace an yi mata yadda aka yi wa ‘Yan Kwankwasiyya
- Ba mamaki Jam’iyyar PDP ta shiga Kotu saboda hana ta taron da aka yi
Dazu nan mu ka ji cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta fara shirin ta maka Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a Kotu a dalilin hana su yin wani gangami da su ka shirya a kwanaki duk da dokar kasa ta ba su dama.
A jiya ne Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Jam’iyyar PDP na shirin shiga Kotu da Gwamnatin Jihar Kano na hana ‘Ya ‘yan su yin wani taro a karshen makon jiya. PDP ta shirya wani taro ne a Garin Gaya amma aka hana su.
KU KARANTA: Tun Kwankwaso na 'Dan makaranta na fara siyasa - Ganduje
Shugaban Jam’iyyar PDP na Kano Alhaji Masud El-Jibril Doguwa ya bayyana wannan a Ranar Juma’a. PDP ta shirya yin gangami ne domin karbar wani tsohon ‘Dan takarar Gwamna a karkashin PDM zuwa Jam’iyyar adawar.
Masud El-Jibril Doguwa yake cewa sun shirya taron su bayan Jami’an tsaro sun ba su izini amma daga baya aka dakatar da su. Jam’iyyar tace an yi mata irin abin da aka yi wa ‘Yan Kwankwasiyya ne a Jihar Kano kwanakin baya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng